September 16, 2026

Tallafawa Marayu Zai Magance Matsalolin Da Muke Ciki -Dr. Kazaure

0

Daga Abdullahi Alhassan Kaduna.

Wani Malamin addinin Musulunci Sheikh Dr, Abdulkadir Sale Kazaure, yace tallafawa Marayu da Mata da marasa Karfi,zai magance matsalolin da muke ciki a fadin Kasar nan,kama daga kunci rayuwa dama matsaloli na yau da kullum.

Sheikh Abdulkadir, Sale, ya ce mutukar dai ana samun mawadata na taimakon wanda basu dashi Musamman ma ,Marayu da marasa Karfi to Lallai talauci dake cikin Al’umma zai ragu, haka Allah zai yaye wa wan nan al’ummar damuwa ko wacce iri ce.

Dr, Sale yana wan nan jawabi ne a taron raba kayayyaki abinci da Sutura na Marayu dake a fadin kananan hukumomi 23 dake Kaduna,a farfajiyar Masallacin tunawa da Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da kawo Kaduna.

Babban Shehun Malamin wanda har ila yau shine Kwamishinan dundundin na Ma’aikatar harkokin Shari’a na jihar Jigawa ,ya kara da cewar, Allah ya umurce mu da mu taimaki Marayu a cikin Ayoyin Alkur’ani mai girma.

“Wan nan yasa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama,ma ya tashi a matsayin Maraya ,to Lallai ne shugabanni da ma dai -dai kun Mutane masu hannu da shuni da su kula da Marayu a cikin al’umma, haka zai sa a rage matsaloli da muke ciki a hankali yanzu.

Tun da farko a nashi Jawabin, Shugaban Kula da Kwamitin Marayu na Kungiyar Jama’atul lzalatul Bidi’a na Jihar Kaduna, Mallam Ibrahim Abdullahi lkara, yace yayi ” kamar yarda kuke gani muna rabon kayan Abinci ne ,ga Ƙananan hukumomin Jihar Kaduna,23 inda muke mika kayayyakin tallafin ga Wakilinsu.

Mallam lbrahim ya kara da cewar,akwai kayan abinci kamar shinkafa 320,Suga Buhu 20,Taliya katan-katan ,kayan sawa ko Sutura da suka hada da Yadika, atamfofi, don dinkawa a Bikin Sallah wanda hakan zai sa suma suyi sallah cikin Farin ciki kamar kowa.

Daga kashe yayi kira ga Jama’a da suriga kwankwasa gidan marayu don sanin halin da suke ciki don tallafa masu, kamar yarda Allah ke cewar Kutuna da Marayu watakila ma zaku Mutu ku bar su kuma Allah zai kawo masu musu tallafawa bayan ba ranaku.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *