Gombe: Abun Mamaki Da Sunan Goje Ya Bayyana Kan Kuri’ar PDP A Zaben Fidda Gwani..
A ranar Litinin din nan ne wakilan jam’iyyar PDP a jihar Gombe suka cika da mamaki, yayin da sunan dan takarar Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC, Danjuma Goje, ya bayyana a takardar zaben PDP. takardun gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar na shiyyar.
Idan dai za a iya tunawa a ‘yan kwanakin nan an yi ta yada jita-jitar cewa Sanata Goje zai fice daga jam’iyyar APC ya sake tsayawa takarar kujerar Gombe ta tsakiya a jam’iyyar PDP sakamakon rikicin siyasar da ke tsakaninsa da gwamnan jihar Inuwa Yahaya.
Majiyarmu ta LEADERSHIP ta ce, hedikwatar jam’iyyar APC ta kasa ta hanyar kwamitin sulhu ta sasanta jiga-jigan jam’iyyar biyu, lamarin da ya sa Goje ya sauya sheka.
Amma a ranar Litinin din nan yayin zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP, sunansa ya bayyana a matsayin daya daga cikin masu neman kujerar Sanatan Gombe ta tsakiya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
A halin da ake ciki, Goje ya samu kuri’u 66 da aka kada inda Abubakar Aliyu ya samu kuri’u 59.
Saidai kuma a wani labari da jaridar VANGUARD ta fitar da misalin karfe 10:05 na daren Litinan, Gojen ya musanta shiga cikin zaben fidda gwanin jam’iyar PDP.
Yana mai bayyana cewa, shi har yanzu cikakken dan jam’iyar APC ne.
