APC Ta Sake Canza Jadawalin Zaben Fidda Gwaninta.
Jam’iyyar APC mai mulki ta sake sauya jadawalinta da jadawalin gudanar da zabukan fidda gwaninta na gwamnoni, ‘yan majalisun Jihohi, ‘yan majalisar dattawa da na wakilai.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa Felix Morka ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Litinin din nan, inda ya ce kwamitin tafiyar da al’amiran jam’iyyar APC ne ya amince da yin wannan sabuwar bitar a taron da ta yi jiya Litinin.
Sanarwar ta kuma kawar da halartar manyan wakilan masu zabe biyo bayan kin amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kudurin dokar zabe ta 2022, wanda zai fadi irin rawar da wannan wakilan masu zaben zasu taka.
A cikin jadawalin da aka yi wa kwaskwarima, za a gudanar da zaben fidda gwani na gwamnoni a ranar Alhamis 26 ga watan Mayu, inda wakilan jihohi kawai za su kada kuri’a.
Jaridar VANGUARS ta ce, a rana guda ne za a gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan majalisun jihohi, amma wakilan kananan hukumomi ne zasu kada kuri’a.
Washegari, wakilan kananan hukumomi suma za su kada kuri’a a zaben fidda gwani na ‘yan majalisar dattawa da kuma zaben fidda gwani na majalisar wakilai a ranar 28 ga Mayu.
Jam’iyar APC ta kara da cewa “Za a gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa kamar yadda aka tsara a ranar Lahadi, 29 ga Mayu zuwa Litinin, 30 ga Mayu, 2022.”
