September 18, 2026

Gidauniyar Aminu Bello Masari: Mutum 1,400 Ne Suka Amfana Da Gyaran Idanu Kyauta Daga Yankin Funtua..

0

An kaddamar da shirin gyaran idonsu kyauta a babbar asibitin garin Funtua, wanda ya hada kananan hukumomin, Funtua, Sabuwa, Dandume, Faskari, da kuma Bakori.

Yayin da aka kaddamar da ashirin a gudumar Malumfashi a babbar asibitin garin wanda ya hada kananan hukumomin Malumfashi da Kafur da Musawa fa Matazu da kuma Kankara.

A jawabinsa yayin gudanar da aikin gyaran idon, Dan kwamitin amintattun gidauniyar wanda ya kula da gyaran idon a yankin karamar hukumar Funtua, Alh. Abdulwahab Funtua ya bayyana cewa” yadda tsarin gyaran idon yake da yadda ya kasance.

Inda yace mutum dari bakwai ne Gidauniyar ta tsara zata dauka domin yi masu gyaran idon, mutum dari uku daga ciki za a basu magani, sai wasu mutum dari uku daga ciki za a basu gilashi, yayin da mutum dari daga cikin su za ayi masu tiyata.

Ya kara da cewa duk da cewa mutum dari bakwai ne Gidauniyar ta tsara zata duba, amma kuma sama da mutum dubu daya su kazo domin duba idanuwan nasu. Amma duk da haka likitocin sunyi kokari wajen ganin duk wanda yazo bai koma haka nan ba.

Daga karshe ya yi kira” ga Al’umma musamman masu hannu da shuni dasu shigo cikin wannan gidauniya su bada tasu gudumuwar domin tallafa ma, al’umma duba masu fama da lalurar su na dayawa, kuma mafi yawansu basuda halin zuwa asibiti domin ayi masu magani.

Haka zalika shima Dan kwamitin amintattun gidauniyar wanda ya kula da aikin gyaran idon a yankin karamar hukumar Malumfashi Alh. Abdullahi Imam ya bayyana cewa” mutum dari biyu su ka tsara zasu yima aiki a yankin, amma sama da mutum dari hudu su ka samu sunzo.

Ya kara da cewa” duk da cewa sun samu yawan abinda sukayi tsari, amma sunyi kokarin ganin duk wanda yazo ko yaya ne, an duba shi, an samu abinda aka ba shi don kada ya koma haka nan, duba da wasu sunzo daga wajen karamar hukumar Malumfashi.

Wadanda su ka amfana da tallafin gyaran idon, sun nuna farin cikinsu da godiyarsu ga Gidauniyar, inda su kace” basu iya tantance farin cikin da sukeji a cikin zuciyarsu, sakamakon rabasu da wannan lalura da akayi.

Daga karshe sunyi addu’a, Allah ya kara daukaka wannan gidauniya.

Mobile Media Crew

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *