Gwamna Masari Ya Baiwa Iyalan Sojan Da Ya Rasa Ransa A Harin Magama Jibiya Kyautar Miliyan Daya
Daga Anas Suleiman Kofar Bai
Baban sakataren tsaro na ofishin gwamnan jihar Katsina, Alhaji Suleiman Yakubu Safana ya jagoranci wani kwamiti domin ziyarar ta’aziya ga iyalan Sojan da yawa rasa ransa tare da duba wanda ya samu rauni.
Wannan kwamiti dai na da nufin kai wani tallafi daga gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ga iyalan mamacin da kuma duba wanda ya samu rauni lokacin da da ‘yan ta’ada suka kai farmaki a magama jibiya a makonin da suka wuce.
Haka kuma wannan tawaga ta mika gudunmuwar naira miliyan daya ga iyalan Sojan da ya rasa ransa tare da bada naira dubu dari biyu da hamsin da ga wanda ya samu rauni domin kula da lafiyarsa.
Daga cikin wadannan suka rufawa tawagar baya akwai shugaban sojoji na 17 Briget da ke Katsina
Anasa jawabin Shugaban Sojin 17 Birget wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan shugaban Sojijin 17 Birget Da ke Katsina, ya nuna jin dadinsa da wannan kulawa da gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Aminu Bello Masari na taimakon bayin Allah.
Daga karshe ya yi addu’a samun zaman lafiya a jihar Katsina da kasa baki daya.
