September 18, 2026

“Faliha & Falisha”: Fim Ɗin Hausa Na Farko Da Za a Nuna A Wasu Manyan Sinimomin Nijeriya 

IMG-20250330-WA0007

 

Faliha & Falisha”: Fim Ɗin Hausa Na Farko Da Za a. nuna A Wasu Manyan Sinimomin Nijeriya 

DAGA MUKHTAR YAKUBU
A yanzu haka dai shirye shirye sun yi nisa na fara haska gawurtaccen fim ɗin nan mai suna” Faliha & Falisha” wanda tsohuwar jaruma kuma furodusa Mansurah Isah ta ɗauki nauyin shiryawa
Fim ɗin wanda ake sa ran za a fara haska shi a manyan Sinimomin Nijeriya a ranar 2 ga Afrilun nan za a nuna shi ne a manyan Sinimomi kamar Platinum da ke Kano, Silverbird Kaduna, Silverbird Jabi, Dex View Kano, Dex View Katsina, Mees Palace Jos (TBC) Alinco Cinema Ijaye Lagos,  Bridge Park Cinema Kaduna, da sauran Sinimomi da ke faɗin tarayyar Nijeria.
Domin ganin yadda haska fim ɗin ya zo da wani sabon salon haskawa da ba a taɓa samun irin sa ba a masana’antar finafinai ta Kannywood, wakilin mu ya tattauna da mai ɗaukar nauyin shirin wato Mansurah Isah inda ta bayyana mana yadda fim ɗin ya samo asali da kuma dalilin da ya sa ta samar da hanyar nuna shi a Sinimomi da yawa a lokaci guda,. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.
Tambaya:  Mun samu labarin a nan gaba kaɗan za ki saki sabon  fim ɗin ki ‘Faliha & Falisha’ ta hanyar nuna shi a Sinimomi masu ya a Ƙasar nan.
Amsa:  To kamar yadda aka sanni dai ni Mansurah Isah ‘yar fim ce tsawon lokaci da na kasance tsohuwar jaruma kuma ni furodusa ce da kuma bayar da taimako ga mabuƙata a ƙarƙashin gidauniyata ‘Today Lefe Foundation’ nake yi.
Kuma ina gudanar da harkokin kasuwanci na a ƙarƙashin kamfani na Today Lefe Production wanda ya haɗa da harkar fim da kuma sauran kasuwancin da nake yi. Haka nan ni Ambasada ce ta kamfanoni da dama.
To shi wannan fim ɗin na ‘Faliha & Falisha’ na yi tunani a kan zan sake shi a You tube ne da kuma bin hanyar haska shi a manyan gidajen talabijin, don haka ba ni da wani tunanin zan haska shi a Sinimomi.
To amma da yake ni mai harkoki ce da mutane da yawa, sai na samu wani manaja da yake da alaƙa da  Sinimomi , don haka sai ya ce bari ya duba ya gani Sinimomi nawa ne za su iya karɓa don su haska fim ɗin ta yadda za a fara kallon sa a Sinima.
To wannan ne ya bani damar fara shiri tun a baya kuma muka yi tunanin a wannan lokaci ya kamata a ce an fara kallon fim din.
To sai muka duba muka ga a taron bikin Sallah babu wani fim da za a nuna a Sinima, wannan ya sa muka ga ya kamata mu tsara yadda za a nuna shi a bikin Sallah don haka a yanzu mun tsara da a fara haska fim ɗin a Sinima a ranar 2 ga Afrilun nan wanda ya dace ga biyu ga Sallah.
Abin da har yanzu mutane suke magana a game da fim ɗin, na Hausa ne ko na turanci, saboda yadda sunan fim din “Faliha & Falisha” .
To shi dai wannan suna  Faliha & Falisha, ya samo asali ne daga wani ɗa da na rike wanda ni na yi masa aure ma  a shekarun baya kuma a yanzu yana zaune a ƙasar Libya da matar sa, to Allah ya nufe su da haihuwar ‘yan biyu sai aka yi musu laƙabi da wannan sunan Faliha & Falisha, to wannan sunan ne ya yi mini daɗi, kuma ya zo daidai lokacin da nake ƙoƙarin neman sunan da za a saka wa fim ɗin, kawai sai na ga ya dace na yi amfani da sunan su a fim ɗin, domin ka san duk finafinan da na yi duk sunayen mutane naka saka musu, ko a baya na yi Fanan na yi Akila da sauran su, wannan shi ne asalin sunan fim ɗin. Amma dai fim ne da aka yi shi da yaren Hausa ba da turanci ba.
Tambaya: To shi wannan fim ɗin, me ya bambanta shi da sauran finafinan da kika yi a baya?
Amsa: To abinda ya bambanta su dai yawancin finafinan da nake yi na kan taɓo abubuwan da suke faruwa a rayuwa ta zahiri, har ya zama mutane suna cewa ni fim ɗina idan aka kalla sai an yi kuka saboda labarin tausayi da nake kawowa.
To sai na ga a yanzu bari na ɗan canza salo, don ya zama fim ɗin ya tafi da nishaɗi don a baiwa masu kallo dariya, amma dai duk da haka labarin fim ɗin wanda ya faru ne da gaske, kuma zai taɓa zuciyar masu kallo, domin ya kawo abubuwan da suka faruwa a rayuwar mu ta wannan lokacin, don haka a wannan Fim ɗin  mun fito da kwarewar mu don mu nuna cewa ba a ɓangare ɗaya kawai muka tsaya ba, muna da kwarewar da duk inda muka taɓo na rayuwar al’umma za mu bada tamu gudummawar.
Mansura isah Furudusan Fim ɗin
Tambaya: Ganin cewar shi wannan fim ɗin na daban ne a cikin finafinan da kika yi, ko wanne irin buri kika ɗaukar wa fim ɗin?
Amsa: To ni gaskiya ba wani buri na ci a kansa ba sai don na faɗakar tare da wayar da kan jama’a a game da irin matsalolin rayuwa da kuma yadda za a warware su. Kuma cikin taimakon Allah sai na samu damar da zan  haska shi a Sinimomi masu yawa, wanda hakan zai sa jama’a masu yawa su kalle shi a lokacin guda, kuma kamar yadda ka sani ne, wannan shi ne fim ɗin Hausa na farko da ya samu wannan damar ta a nuna shi a Sinimomi masu yawa a lokaci guda, kuma gaskiya na ji daɗin wannan.
Babu abin da zan ce wa Allah sai godiya ina fatan wannan nuna fim ɗin ya zamo buɗewar wata kofa ta haska finafinan Hausa a Sinimomi masu yawa nan gaba ta yadda su ne za su rinƙa zuwa suna nema a wajen mu don su haska a Sinimomi su.
Don haka ina son abokan sana’a ta su bani haɗin kai domin samun nasarar wannan fim ɗin samun nasarar mu ce gaba ɗaya , domin idan ya karɓu zai buɗe wata hanyar samun kuɗi, ba ga fim ɗin ‘Faliha & Falisha’ ba kadai ba, har ma da finafinai masu zuwa a masana’antar finafinai ta Kannywood, don haka ina fatan za mu haɗu don yaɗa fim ɗin tare don ya samu karɓuwar da zai ƙara buɗewa sauran finafinai hanyar Kasuwanci.
Kuma ina fatan masoyan mu Hausawa da waɗanda suke jin yaren Hausa Sinimomi sun yi mana kukan mu Hausawa idan mun je Sinima ba ma kallon fim ɗin Hausa, ko da an saka  sai su ce su ba za su kalla ba.
To gaskiya dole ne mu so namu, domin mu tabbatar muna son yaren Hausa da kuma kishin sa, don haka mu bayar da goyon baya don mu ba marar da kunya a wannan lokacin mu nuna musu muna da zuciya.
Mu kalli ‘Yoroba Films’ daga an sake shi, Bayerabe da yake Landan zai je ya kalla. Haka shi ma Ibo, fim din  yaren sa zai je ya kalla.
To mu me ya sa ba ma yin hakan? Ba ma yin kishi lokaci ya yi da za a ce Bahaushe ya koma kallon finafinan yaren sa, don ya nuna yana da kishin yaren Hausa. Muna fatan za mu samu goyon baya da haɗin kai.
To Madalla mun gode
Nima nagode Sosai.

About The Author