Martani: Babu Wata Badaƙalar Kuɗi Ta Naira Miliyan 407 A Hukumar Sufuri Ta KTSTA Katsina
Martani: Babu Wata Badaƙalar Kuɗi Ta Naira Miliyan 407 A Hukumar Sufuri ta KTSTA Katsina
Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Katsina (KTSTA) ta mayar da martani kan zargin bacewar kudade har Naira miliyan 407 a hukumar, kamar yadda wata kafa ta watsa labarai ta yanar gizo ta yi zargi, bisa wani rahoto da ofishin Mai Binciken Kudi na Jihar ya fitar.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar ta KTSTA, Musa Sa’idu ya bayyana cewa an samu badakalar bacewar kudaden ne tun a shekarar 2016 kafin a nada shuwagabannin hukumar na yanzu.
“Kudaden da aka kashe ba bisa ka’ida ba na Naira miliyon 407 da kuma kudaden shiga da ba a san inda aka kai su ba na Naira miliyon 24, wanda a karshen binciken aka bada ummarnin masu kula da tattara kudin da su mayar da kudin acikin asusun hukumar ta KTSTA.
“A shekarar 2018 ne aka nada Haruna MusaRugoji a matsayin Shugaban Hukumar Sufuri ta KTSTA, Sakamakon chanjin wurin aiki da suka samu shida Hon Babangida Nasamu.kuma tun lokacin da aka nada shi ba a samu rahoton badakalar kudi a hukumar ba”, inji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa a lokacin da Haruna Musa Rugoji ya amshi jagorancin hukumar KTSTA a shekarar 2018, ya gaji bashin sama da Naira miliyan 50 wanda ya biya duka.
“Basussukan sun hada da albashi da alawus din ma’aikatan KTSTA, da basussuka na dillalan motocin da kanikawa da masu sayar da kayan motoci da sauransu.
“Hukumar ta kuma gaji motoci 106 amma guda 57 ne kadai ke aiki, sauran duk a ajiye suke saboda lalurori daban daban, amma a yau, duk motocin KTSTA suna aiki kuma suna samar da kudaden shiga ga Hukumar kamar Yanda doka ta tsara.
Har ila yau sanarwar ta bayyana cewa shugabancin mai ci a hukumar ta bullo da wani Tsari na hadin gwiwa tsakanin Hukumar da masu zaman kansu wanda ya kara samar da kudaden shiga ga hukumar ta KTSTA.
“A yau hukumar KTSTA tana tafiyar da budadden asusu inda duk abin da take samu a lissafe yake, kuma gwamnati ta san inda kudin ke tafiya.
“Hukumar na tafiyar da asusunta bisa tsantseni da gujewa almubazzaranci ko almundahana, bisa tsarin gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa.
“Cikin kudaden da take samu har ma ta fara bude sabbin tashoshi a wasu sassan jihar domin ta saukake zurga-zurga ga matafiya a kowane sashen na jihar”.
Sanarwar ta ce hukumar KTSTA karkashin jagorancin Alhaji Haruna Musa Rugoji za ta cigaba da tabbatar da gaskiya da tsantseni wajen gudanar da asusunta, tare da inganta harkar sufuri ga al’ummar Jihar Katsina.
