Ekweremadu Da Matarshi Na Son Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Ukpo.
Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da uwargidansa, Beatrice sun bukaci babbar kotun tarayya dake Abuja ta yi watsi da bukatar da mai bada tallafin koda David Ukpo ya shigar, inda ya bukaci kotun ta yi watsi da umarnin da ta bayar a ranakun 1 ga watan Yuli da kuma 6 ga watan Yulin, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sunnews.
Ukpo, ta bakin lauyansa, Bamidele Igbinedion, ya shigar da kara a gaban kotun, inda ya bukaci mai shari’a Inyang Ekwo da ya yi watsi da umurtar wasu hukumomin gwamnati da bankuna su saki bayanansa ga Ekweremadu da matarsa.
Ukpo, wanda a halin yanzu yana kasar Burtaniya dangane da tuhumar da ake masa na karbar gabobin jiki da ake zargin Ekweremadu, ya bayyana cewa amincewa da bukatar ma’auratan ya keta hakkinsa na sirri da sashe na 37 na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999.
Sai dai a wata takarda ta kara da Bright Ekweremadu, kanin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan, wadanda suka nemi ya yi watsi da shi, ya ce Ukpo ba shi da hurumin hakan saboda doka ba ta amince ba.
Takardar mai lamba FHC/ABJ/CS/984/2022 na dauke da sa hannun lauyansuAdegboyega Awomolo SAN da kuma kwanan watan da ya shigar da ƙara ranar 8 ga watan Satumba.
A cikin muhawara mai maki 20, Ekweremadu ya yi watsi da cewa duk da kotu ta yanke hukuncin a ranar 1 ga watan Yuli, amma ba a keta hakkin Ukpo na yin adalci ba.
