Duk Arewa Babu Inda Jam’iyyar APC Take Zaune Lafiya Kamar Jihar Kebbi – Bagudu
Kaf Din Jihohin Arewa Maso Yammacin Najeriya Babu Inda Jam’iyyar APC Take Zaune Lafiya Kamar Jihar Kebbi, Wannan Ya Biyo Bayan Adalcin Kyakkyawan Jagorancin Irin Mai Girma Gwamnan Jihar Kebbi Sen, Atiku Bagudu (“Matawallen Gwandu”) Shugaban Gwamnonin Jam’iyyar APC Na Ƙasa.
Adalcin Gwamnan Jihar Kebbi Sen, Atiku Bagudu yasa jam’iyyar APC A jihar kebbi take a dunƙule waje daya, Cewar Dr, Hussaini Suleiman Kangiwa (“Sarkin Arawan Kabi”) shugaban hukumar masu buƙata ta musamman ta ƙasa, ko ince shugaban mai kulada hakkin masu buƙata na ƙasa.
A yanzu jam’iyyar APC babu wanda ta aminta da amanarsa kamar Sarkin Arawan Kabi fagen taimakawa ‘Ya’yan jam’iyyar APC da kokarin dada kan ‘Ya’yan jam’iyyar APC shike kan gaba
Comrade Musa Garba Augie, ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattauna wa da manema labarai dangane da jaddawalin zaɓen kananan hukumomin jihar kebbi da za’a gudanar a wata Feburairu na wannan shekarar da muke ciki 2022.
Ni dai bana ganin akwai jam’iyyar ADAWA a jihar kebbi, saboda har’yanzu ba su shiryaba, kansu ba haɗe yakeba, mulura da kyau rarrabuwar kawunan dake tsakaninsu shi yasaka mun wannan shakku, hakika ina shakkun shigarsu zaɓe saboda matsalolin da suka dabaibaye su a halin yanzu.
Babban sakona ga Yaƴan jam’iyyar APC shine muzama tsinstiya madaurinki daya kamar yadda aka sanmu da haƙuri da juna, mulki na Allah ne shike bada shi ga wanda yaso lokacin da yaso.
