Dan Takarar Jam’iyar PRP Na Kankia-Kusada-Ingawa Ya Shuwarci Mutane Su Guji Saida Katunan Zaɓensu.
Dan takarar jam’iyar PRP da zai wakilci Kankia-Kusada-Ingawa a mazabar tarayya ya shawarci mutane su tabbatar da ganin sun amshi katunan zaɓensu na dindindin.
Kabir Umar Abdullahi wanda aka fi sani da Mairawani ya bada wannan shawarar ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina.
Dan takarar wanda ya bukaci mutane su guji saida katunan zaɓen su, ya ce da shi ne kaɗai hanyar zabar zabar shugabannin da suka kwanta masu a rai.
Kabir Umar Abdullahi wanda ya shawarci yan siyasa akan su guji siyasar a-mutu-ayi-rai, ya bukace su da suyi siyasar da zata taimaka wajen ɗorewar demokradiyya.
Hakanan kuma, ya yaba ma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da hukumar zaben kasar akan bada tabbacin gudanar da sahihin zabe.
Sannan ya roki mutane su zama masu bin doka da oda a lokacin, da kuma bayan kammala zabe, tare da yin addu’ar ganin an gudanar da zaben lami lafiya.
