September 17, 2026

Dalilin Da Yasa Muka karrama Kamfanin Green House Katsina – Kungiyar NUJ Katsina

0

A jiya Lahadi ne kungiyar’yan jarida ta ƙasa reshen jihar Katsina suka karrama daya daga cikin hamshakan ‘yan kasuwa na garin Katsina bisa wasu dalilai da kungiyar ta bayyana.

Kamfanin Green House Enterprises Katsina ya karfi kyautar lambar yabo daga kungiyar gamayyar ‘yan jaridu wata NUJ.

An bayar da wannan lambar yabone da misalin karfe 10:00 na safe a tsangayar Shadda wato Shadda Department, Green House Katsina.

Kungiyar ‘Yan jaridar wadda aka fi Sani NUJ ta miƙa wannan kyauta Mai nuni da cewa kamfanin Green House shine Garzon Wannnan Shekara a Fannin kasuwanci da koyar da sana’o’i.

Wakilan kungiyar ta NUJ da Suka samu halarta sun samu tarbar Director na Green House Katsina Alh. Sani Shehu Namaska (MSc B.A.) manager na Green House Alh. Salisu Shehu, Isah Sani Alh, Ashiru Garba da sauransu.

Green House Enterprises Katsina Na Mika sakon Godiya da bangajiya ga NUJ.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *