‘Yan Bindiga Sun Farmaki Garuruwan Kaduna, Sun Kashe Mutane 7, Sun Sace Wasu Da Dama
Wasu tsagerun yan bindiga sun farmaki al’umma a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna Maharan sun halaka mutane bakwai sannan suka yi garkuwa da wasu mutane 57 Har ila yau sun harbi wani dalibilin ajin karshe na makarantar sakandaren kimiya da ke Birnin-Gwari, yana kwance a asibiti
Yan bindiga sun kai hare-hare a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, sun kashe akalla mutane bakwai sannan suka yi awon gaba da mutane 57.
An tattaro cewa maharan sun farmaki wata mota a Kuriga, hanyar titin Birnin Gwari zuwa Kaduna a ranar Asabar, 26 ga watan Fabrairu. Jaridar The Cable ta rahoto cewa wani dalibin makarantar sakandare ta kimiya da ke Birnin Gwari ya tsere da rauni daga harbin bindiga.
‘Yan bindiga sun farmaki garuruwan Kaduna, sun kashe mutane 7, sun sace 57
Shugaban kungiyar Birnin Gwari Vanguard for Security and Good Governance, Ibrahim Nagwari, a cikin wani jawabi a ranar Asabar, ya bayyana cewa maharan sun kuma farmaki mazauna a Unguwar Bula, Unguwar Dafillo da Ijinga a karamar hukumar Randagi.
A yau da misalin karfe 10:00 na safe, wani dalibin ajin karshe na makarantar sakandaren kimiya ta Birnin-Gwari ya tsere da raunin harbi a kafadarsa a hanyarsa ta zuwa yin rijistan JAMB/UTME a Kaduna.
“Yan fashin sun bude wuta kan motar da dalibin da sauran mutane ke ciki a kauyen Manini bayan Kuriga a hanyar titin Birnin-Gwari Kaduna. “
Dalibin yana jiran ayi masa tiyata domin cike harsahin daga kafadarsa a babbar asibitin Jibrin Maigwari da ke Birnin-Gwari. “Hakazalika, yan bindigan sun kashe mutane bakwai a Unguwar Bula, Unguwar Dafillo da Ijinga da ke yankin Randagi, Birnin-Gwari a ranar Asabar.
“Yan bindigar a kan babura kimanin su hamsin sun farkami garuruwan da misalin karfe 11:00 na sadiyar Juma’a sannan suka shafe tsawon awa hudu, inda suka hana mutane yin sallar Juma’a.
Yan fashin, baya ga kashe mutane shida a nan take, wani mutum daya ya mutu a safiyar nan a babbar asibitin Jibrin Maigwari, yayin da aka sace wasu 57 wanda da damansu mata ne duk a wannan garin
