Dalilin Da Yasa Motocin Yan Sanda Suke Kaca-kace, Raga-raga – PRO.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana dalilin da ya sa motocin sintirin da jami’an ‘yan sandan ke amfani da su ke yin raga-raga kuma kaca-kaca
Wannan bayanin ya zo ne a matsayin martani ga wani mai amfani da shafin Twitter wanda ya tambayi dalilin da ya sa motocin ‘yan sanda ke zama cikin irin wannan halin.
Kamar yadda Adejobi ya bayyana, yawan sa’o’in da motocin ke kwashewa a kan titin domin yin aiki ke sanyawa suna zama cikin irin wannan yanayin.
Mai amfani da shafin na Twitter dat_Afikpo boi @sparoswagg ya rubuta “Abeg wetin dey always skata the hilux wey dem dey give una?” domin maida martani ga hotunan da Adejobi ya ɗora akan shafin Twitter na sabbin manyan motocin aiki da za a yi amfani da su gabanin babban zaɓen dake tafe.
A martanin da Adejobi ya bayar ta shafin Twitter: “Duba, motocin sintiri na ‘yan sanda suna aiki awanni 24. Lokacin da kuka ajiye motarku ta gida da yamma, a lokacin ne wata tawagar jami’an yan sandan za ta karɓi abin-hawan aka yi amfani da shi da safe domin yin sintiri cikin dare. Motocin aiki ba za su iya zama masu kyau kamar motocin gida ba. Dukkan abubuwan da ake aiki da su zaka gansu kace -kace, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Vanguard.
“Saboda haka, wahalhalun da motocin yan sanda ke sha ke sa su yin raga-raga da kace-kace. Da damar suna hawan hanyoyi marasa kyau. Saidai a kowane lokaci muna karfafa gwiwar DPO da sauran shugabannin sassan yan sanda su riƙa kula da lafiyarsu.”
