‘Yan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Kitsa Yin Garkuwa Da Mahaifinsa A Kwara.
‘Yan sanda a jihar Kwara sun kama wani mutum mai suna Issa Naigheti, wanda ake zargi da hada baki da wasu mutane biyu wajen yin garkuwa da mahaifinsa.
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar dake yaƙi da masu garkuwa da mutane suka kama Naigheti a ranar 4 ga watan Janairun shekarar 2023 a Kambi kan babbar hanyar Ilorin zuwa Jebba a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce wanda ake zargin a lokacin da ake yi masa tambayoyi ya amsa laifin hada baki da wasu mutane biyu wajen sace mahaifinsa.
“Jami’an rundunar ‘yan sanda dake yaƙi da masu garkuwa da mutane ne suka kama mutanen mai suna Issa Naighet a ranar 4/1/2023 a kusa da unguwar Kambi dake Ilorin yayin da suke bibiyar sahun masu garkuwa da mutane; A lokacin da ake tattaunawa da shi ya bayyana cewa ya haɗa baki da wasu mutane biyu wajen sace mahaifinsa, kuma an karbo kudi naira miliyan 2.5 a matsayin kudin fansa.
Ana ci gaba da kokarin damke sauran wadanda ke da hannu a lamarin, kuma za a mika su zuwa jihar Oyo, inda aka aikata laifin, a cewar majiyar jaridar Popular News Hausa ta jaridar Leadership.
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar ya sake nanata kudurin sa na samar da ingantaccen tsaro domin gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali,” in ji mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar.
