November 18, 2026

Corona: Shugaba Buhari Ya Nuna Jin Dadinsa Akan Cigaban Da Aka Samu Na Samar Da Ruwan Allurar A Afrika

0

Daga Auwal Isah

Shugaban kasar ya fadi hakan ne a Brussel dake kasar Belgium yayin da yake bada gudunmuwarshi a wurin zaman tattauna na kula da lafiya da samar da rigakafin cutar Corona a lokacin taron kashashen Afrika da na turai a karo na 6.

Shugaban kasar ya bayyana jin dadinshi bisa saka Najeriya a cikin kasashen da za su amfana da fasahar samar da ruwan allurar.

Kamar yadda ya ce, Najeriya na daya daga cikin kasashen nahiyar Africa da suka maida hankali wurin samar da rigakafin cutar, da kuma masayar fasahar zamani.

Ya ce Najeriya ta kuma bada damar amsar bakuncin taron bada horo na hukumar kula da lafiya ta duniya.

Shugaban kasa Muhammad Buhari wanda ya yi kira da a yi hadin gwiwa don shawo kan annobar cutar ta Corona, ya yaba ma kungiyoyi da hukumomin bada tallafin kasashe waje bisa samar ruwan allaurar rigakafin cutar.

Haka kuma, shugaban kasar ya yi kira da a yi hadin gwiwa da kungoyar tarayyar turai don magance tasirin cutar a nahiyar Afrika

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *