November 18, 2026

Makarantar Firamare Unwala Jan-Gefe Na Cikin Halin Ni ‘Ya su A Katsina

0

Daga Abubakar Isah Hassan

Unguwar Unwalar Jan-gefe da ke bayan Jami’ar Alqalam Katsina tana ɗaya daga cikin manyan unguwanni masu tasowa cikin sauri a jihar Katsina.

Akasarin mazauna yankin talakawa ne da masu matsakaicin ƙarfi da ke gudanar da harkokin su gwanin ban sha’awa ta hanyar dogaro da kai da kuma ayyukan gayya na raya Unguwar.

Wannan dalilin ne yasa suka sama wa yaran su makarantar firamari ta wucin gadi da kwaɗayin shigowar gwamnati domin share musu hawayen su, inda suka riƙa zarya a tsakanin karamar hukumar Batagarawa da ma’aikatar Ilimi a ƙarƙashin jagoranci Mal Ibrahim Isah da Malama Zulaihat S Turare.

Haka kuma Magaji Jino ma ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin yankin ya sami makaranta, daga bisani gwamnatin ta shigo ta kawo Headmaster da Malamai kuma aka ci gaba da karatu da alƙawarin za’a gina musu makaranta ta dindindin.

Da fari wani bawan Allah ne ya bada aron gidan Kajin sa wanda bai kammala ba ake karatun daga bisani kuma ya tayar da su a karo na biyu bayan da fari Magaji Jino yazo ya nemi alfarma ya ƙara musu wa’adi, bayan ya ƙara wa’adin na term guda sai ya tayar da su tare da ƙorafin shima zai ci gaba da aikin sa ne domin yaga gwamnati bata niyar samar wa yankin da makaranta ta dindindin.

Haka aka cigaba da fadi tashi inda har daga bisani Malama Zulaihat tare da shawarar ƴan unguwar ƙarƙashin jagoranci Mal Ibrahim ta ba su wani kangon gidan ta da ta fara ginawa mai ɗakuna ukku bayan da ta yi ƙoƙarin biga masa kwano, domin suci gaba da karatun ita ma kafin ta nemi a bata wurin ta.

Na kai ziyara a makarantar kuma sai da na kusa na zubar da ƙwalla ganin halin da Malamai da ɗaliban makarantar ke ciki.

Haƙiƙa suna takure sosai babu mai iya miƙe Ƙafar sa saboda cin koso suna zaune cikin kasa babu tabarmin kirki bare ayi batun kujeru.

Malaman na tsaye suna ƙoƙari kowa na ta zufa kamar lokacin bazara na faɗi a raina haƙiƙa yanda na nasan mai girma gwamna a fannin harkar ilimi to kuwa zai yi wuya ace yasan halin da bayin Allahn nan suke ciki?

Na zanta da wasu daga cikin mutanen Unguwar sun nuna irin damuwar da suke ciki akan rashin makarantar basu san me gobe zata yi ba idan har ita mai wurin ta buƙaci wurin ta kamar yanda na fari yayi.

A zantawa ta da ɗaya daga cikin waɗanda suka dage ganin an samar da makarantar Mal Ibrahim yace suna kira da kai kukan su ga mai girma gwamnan Aminu Bello Masari da ya kawo musu ɗauki domin suna da yaƙinin cewa bai san halin da yaran su suke ciki ba.

Musamman idan aka yi la’akari da yanda yake bakin ƙoƙarin sa wajen gani ya agaza wa harkar ilimi a jihar ta Katsina.

Yace yanzu haka ma idan har wannan zangon na karatu ya ƙare basu san yanda zasu yi ba domin ɗakuna ukku ne gare su kuma suna da ɗalibai sama da 500 firamari 1 da 2 kaga kenan babu batun ƙara ɗaukar yara domin waɗanda ke ciki ma abubuwan sunyi musu kaɗan matuƙa, ya ƙarƙare.

Ina roƙon mai girma gwamna Alh Aminu Bello Masari da gwamnatin sa mai adalci da ya dubi halin da unguwar nan take ciki da idon rahama ya sama wa wannan unguwa makaranta ta zamani domin haskaka goben yaran su.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *