Buhari Ne Ya Fito Da Ƙima Da Darajar Manoma A Nijeriya. inji Kungiyar Manoma Ta AFAN
Kungiyar Manoma ta Ƙasa reshen jihar Katsina ta bayyana tsohon shugaban Kasar Muhammad Buhari a matsayin wani gwarzo wanda tsare-tsaren gwamnatin sa ne suka fito da ƙima da kuma martabar manoma a Nijeriya.
Shugaban Kungiyar a jihar Hon. Ya’u Umar Gwajo-Gwajo ya bayyana haka a lokacin da kungiyar ta kaiwa tsohon shugaban Kasar ziyarar ban girma a gidan sa da ke Daura.
A cewar sa, tsare-tsaren da gwamnatin shugaba Buhari ta zo da su a ɓangaren noma sun taimaka matuƙa gaya musamman manoma na cikin gida sun amfana da wannan tsari saboda haka ne manoma sun zama sarakai a yanzu ta dalilin haka.
Hon. Ya’u Umar Gwajo-Gwajo ya ce duk wani manomi a ƙasar nan yana cikin rufin asiri, amma a cewar sa, ba mai gane wannan kokari da shugaba Buhari ya yi sai mai hankali da tunani zai gane tasirin tsare-tsaren gwamnatin sa a harkar noma.
Haka kuma ya bayyana cewa ada jihar Katsina babu injinan casar shinkafa, yanzu kuwa har katafaran kamfanin casar shinkafa ke akwai wanda shi shugaban ƙasa ya bude da kansa, kuma yana samar da shinkafa yadda ya kamata a jihar Katsina da wasu jihohin Nijeriya.
Hon. Ya’u Umar wanda ya samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin kungiyar na jiha ya bayyana dalilin kawo wannan ziyara, inda ya ce sun zo ne akan batutuwa masu muhimmanci guda biyu.
‘Mai girma tsohon shugaban Kasa, mun zo tayaka murna ka gama mulki lafiya ka dawo gida, lallai muna yi wa Allah godiya akan wannan ni’ima da ya yi mana na samunka a matsayin shugaban ƙasa wanda ya san ciwon manoma ‘ inji Gwajo-Gwajo
Shugaban kungiyar ya ƙara da cewa batu na biyu da ya kawo su shi ne, neman shawara da tabaraki daga tsohon shugaban ƙasar musamman abubuwan da suka shafi yadda za su ƙara inganta harkokin noma da kiwo a wannan yanki na arewa.
Kazalika kungiyar ta naɗa tsohon shugaban kasar a matsayin uba kuma jigo a ƙungiyar manoma ta AFAN reshen jihar Katsina.
A nashi jawabin tsohon shugaban ƙasar Muhammad Buhari ya nuna jin daɗinsa da wannan ziyara inda ya karfafa masu gwiwa da
cewa duk abinda ake nema na duniya na cikin sha’anin noma da kiwo.
Shugaban ya bada tarihi irin gwagwarmayar da ya sha a lokacin da yake aikin soja wanda ya ce har gobe baban abinda yake tunkaho da shi, shi ne noma da kiwo domin a cewar sa sune ya gada daga wajan iyaye da kakanni.
Tsohon shugaban ƙasar ya yi fatan cewa manoma a Nijeriya za su cigaba inganta harkar noma domin samar da wadattaccen abinci a wannan lahiya. Daga karshe ya yi fatan Allah ya maida kowa gidansa lafiya tare da rokon Allah ya ba Nijeriya zaman lafiya.
