September 17, 2026

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Sace Mata 23 Da Ma’aikatan Kamfani 10 A Zamfara

0

Daga Hussaini Ibrahim

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mata ashirin da uku a gundumar Damaga da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin mai suna Malam Ahmed Musa Damaga ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da da wakilin mu ta wayar tarho A yau Alhamis.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Laraba da misalin karfe 12:00 na rana alokacin da matan suka je daji debo icen giki.

Hakazalika, ‘yan bindigar sun mamaye garin Talata Mafara hedikwatar karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara inda suka yi garkuwa da ma’aikatan wani kamfanin gine-ginen titi goma da aka fi sani da Triacta.

Malam Aminu Abubakar Mafara ne ya bayyyana ma wakilin mu kwashe Ma’aikatan kamfanin yau a Alhamis.

A cewarsa, sun mamaye garin ne da misalin karfe 11:00 na daren jiya “Yan bindigan suka fara harbe-harbe. sun tafi kai tsaye gidan tsohon dan majalisa mai wakiltar Talata Mafara da Anka majalisar wakilai ta tarayya, Hon. Kabiru Classic.

“Sojoji sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar bayan sun shafe awa daya da rabi suna cikin garin.”

Nayi kokarin samun jinta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ASP. Yazeed Abubakar abun ya ci tura.ya zuwa hada wannan rahotan

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *