Bani Da Burin Da Ya Wuce Na Zama Babbar Jaruma Cewar Safnah Lawal
Sabuwar Jaruma a masana’antar finafinai ta Kannywood, Safna Lawal, ta bayyana burin da take da shi na ta samu daukaka ta zama babbar Jaruma a masana’antar Kannywood.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar da muka yi da ita a game da dalilin ta na shigar ta harkar fim.
Tun da farko dai ta gabatar da kanta da cewar ” Suna na Safna Lawal ni ‘yar cikin garin Kaduna ce a Unguwar Mu’azu aka haife ne a yanzu ina da shekaru 22 a duniya kuma na yi karatuna na firamare da Sakandare, Sannan na yi makarantar Islamiyya har na yi sauka.”
A game da harkar fim kuwa cewa ta yi
“Na tsinci kaina da son harkar fim tun ina karama, har na girma kuma na samu hanyar da na zo Kano, yau kusan shekaru 8 kenan da shiga ta harkar fim, duk da dai a baya da na fara ban dade ba na koma gida sakamakon maganar aure da ta taso da za a yi mini kuma bai yiwu ba sai daga baya na dawo.
Kuma Finafinan da na san fito tun a wancan lokacin akwai Dakta Bahijja, da Sarina, sai Hauwa Kulu. To daga nan ne na koma gida, na samu tsawon lokaci, da auren bai yiwu ba na dawo saboda ina ra’ayin abin Sosai.”
Ko da Safna Lawal ta dawo bayan tsawon lokaci ya ya ta samu masana’antar?
“To gaskiya na samu harkar ta sauya, saboda a wancan lokacin a na yin fim na DVD ne amma a yanzu an koma YouTube channel da gidajen Talbijin, don haka aiki ba irin na baya ba ne, kamar yadda kasuwa ta sauya haka aikin ya sauya.
Amma dai da na dawo na fara aiki ne in da na fito a fun din ‘Yar garuwa kuma daga baya Allah ya sa na samu shiga cikin fim din Izzor so wanda Ahmad da yake a Danbare ya hada ni da Aminu Arrahus har na fito a cikin Shirin Izzor so.
Kuma gaskiya ina jin dadi sosai da kasancewa ta Jaruma a cikin Shirin Izzor so, don fim ne na tarbiyya da fadakarwa, don haka ina jin kaina cikin wani shauki idan na je wajen aikin.”
Mun tambaye ta ko ta samu Matsala a gidan su a game da shigar ta harkar fim?
“To ba zan iya cewa ban samu ba. Na samu gaskiya, don mahaifina ya amince, don shi ma ya tsaya mini,amma sai ya zama wata yayar sa ba ta so, to daga baya dai ya fahimtar da ita.”
Dangane da burin da take da shi kuwa cewa ta yi
” A yanzu babban burin da nake da shi ba ya wuce na zama babbar Jaruma yadda zai zama duniya ta sanni Jama’a kowa ya sanni su na alfahari da ni shi ne babban burin da nake da shi.kuma idan Allah ya ba ni dama buri na ba ya wuce na taimaki Jama’a da kanne na saboda maraici da muka tashi a ciki na mahaifiyar mu wadda tun ina karama Allah ya yi mata rasuwa.
Don haka ina fatan Allah ya cika mini burina kuma ya sa na gama da harkar fim din lafiya.”
