Bamu San Amsar Sabbin Takardun Kuɗi Saboda Suna Mamu Kama Da Na Jabu – Ƴan kasuwa.
Kwanaki shida da fara aikin sabbin takardun kudin Naira, har yanzu wasu ‘yan kasuwa na da wuya su amince da su a matsayin takardar kudi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.
Sabbin takardun kudi na N1,000, N500 da N200 dai, sun zama doka tun a ranar 15 ga watan Disamba, 2022.
Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, a ranar 26 ga watan Oktoba ya bayyana shirin sake fasalin takardun kudi, tare da cewa tsofaffin takardun kudaden ba za su daina aiki ba sai ranar 31 ga watan Janairu, 2022.
Ya ce dalilin da ya sa aka sake fasalin kudin shi ne don a magance jabun kudaden da ake fama da su.
Wata mai sayar da abinci a tashar motar Cele-Egbe, Egbe, Alhaja Sofiat Balogun, ta ce ba za ta karbi sabbin takardun kudaden ba tukuna.
“Mutane sun ce kudin ba su da kyau kuma har yanzu babu su a ko’ina, saboda hakan ba zan karba ba har sai na ga sun game gari.
“Ba na so in fara karbarsu, kuma idan na tashi kashe hakan ta yi man wahala.
“Na biyu kuma, na ga bidiyon wata sabuwar takardar kudaden bogi ta Naira 1000 a kafafen sada zumunta, wannan ya kara sanya ni tsoron karban kudin,” inji ta.
Misis Eme Jackson, wata mai sayar da ’ya’yan itace a kasuwar Ili-ewe, Egbe, ta ce dalilin da ya sa ta ki amincewa da kudin shi ne, takardun sun yi haske sosai.
“Na fi son tsaffin takardun kuɗaɗen, saboda sun fi ƙarko sosai duk yadda za ka sarrafa su, sabbin kudaden ba zasu yi kwari kamar wadanda ke akwai na asali ba.
“Lokacin da na gansu, na faɗa ma ƴaƴa na cewa kada su amshe idan na barsu tsaron kasuwa ta,” in ji ta.
Mista Ozuome Benedict, kwararre kan harkokin waya, ya bukaci babban bankin da ya wayar da kan mutane akan dalilin da ya kamata mutane su yi amfani da shi wajen amsar sabbin takardun kuɗin.
“Ba ni da matsala da karbar sabbin takardun kudin, amma ya kamata babban bankin Najeriya ya wayar da kan jama’a akan batun, saboda da yawan mutane ba su da masaniyar cewa akwai sabbin takardun kudin ba, shi yasa ma basu karbarsu,” in ji shi.
A halin da ake ciki, ziyarar da kamfanin dillancin labaran Najeriya ya kai ma wasu injinan cire kudi na ATM da ke kusa da Ikotun, Ejigbo da Oshodi, ya nuna cewa har yanzu tsaffin kudade ne kwastomomi ke samu a cikin injinan cire kudi idan sun je banki.
A lokacin ziyarar da kamfanin dillancin labaran Najeriyar ya kai ɗaya daga cikin bankunan, wani mai amasa da bada kudi a banki ya ce ma wata abokiyar ciniki da ke son cire Naira 100,000, cewa za a biya ta Naira 20,000 ne kawai na sabbin kudi, sai a bata cikon sauran kuɗin naira N80,000 da tsaffin takardun kudi.
Amma lokacin da abokiyar cinikin ta tambayi dalilin da ya sa ba za ta biya ta gaba ɗaya da sabbin kudin ba, sai ma’aikaciyar bankin ta ce mata, wannan umarni ne aka bata itama.
“Ku yi hakuri za ku iya samun naira N20,000 na sabbin kudi ne kawai, saboda umarni ne da babban bankin Najeriya ya bamu,” inji ma’aikaciyar bankin da ke aikin hadahadar kudaden da abokan ciniki.
Sai dai kuma ziyarar da kamfanin dillancin labaran Najeriya ya kai wa injin cire kudin bankin Zenith, ya lura cewa injin din na raba sabbin takardun kudi na N500 da N200.
Wasu kwastomomin da suka ga sabbin takardun a karon farko, sun bayyana ra’ayoyinsu daban-daban yayin da suke shaida takardun kuɗaɗen a hannunsu, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard.
