‘Yan Sanda Sun Kashe Shugaban Yan Ta’adda Da Wasu 11 A Bauchi.
Wani aikin hadaka karkashin jagorancin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi sun yi nasarar kashe mutane 12 da ake zargin ‘yan bindiga ne a maboyarsu hudu da suka haɗa da Mansur, Digare, Gwana da Dajin Madam dake a dajin Alkaleri a jihar Bauchi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a wannan Litinin ɗin, ya ce shugaban ‘yan ta’addan, Madaki Mansur, wanda ya addabi yankin karamar hukumar Alkaleri, da sauran jihohin da ke makwabtaka da Taraba, Filato da Gombe, an kashe shi a lokacin da jami’an tsaron suka kai samamen.
Wakil ya ce, “A ranar 19 ga watan Disambar 2022 da misalin karfe 02;30am , rundunar hadin guiwa da jami’an tsaro ta fatattaki wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne da masu garkuwa da mutane a maboya guda hudu; Mansur, Digare, Gwana da Dajin Madam a dajin Alkaleri. Biyo bayan musayar wuta da jami’an tsaron suka yi, hakan ya yi sanadin kashe 12 daga cikin masu garkuwa da mutanen, yayin da wasu kuma aka fatattake su, tare da tarwatsa zuwa cikin dajin da ke kusa da wurin, a cewar jaridar DailyTrust majiyar Popular News Hausa Hausa.
“An gano makamai da babura a yayin aikin. Sannan rundunar ta ƙara kaimi domin kamo ‘yan ta’addan da suka gudu.”
