Ba A Samu Korafi A Katsina Ba — Uwar Jam’iyar APC.
Kwamitin karbar korafe korafen da uwar jam’iyyar APC ta kasa ta turo jihar Katsina ya ce ba wani korafi da ya karba dangane da shirye shiryen zaben wakilan da zasu zabin yan takara a zaɓen fitar da gwani na kujerar gwamna.
Shugaban kwamitin Alhaji Musa Shu’abu Gusau ya tabbatar da hakan a lokacin da ya gabatar da wani kwafi na rahoton aikin kwamitin ga gwamna Aminu Bello Masari.
Alhaji Musa Gusau ya yi hasashen cewa kokarin gwamnan jihar na tabbatar da bayar da dama ga kowa ya taimka gaya wurin samun karin yayan jamiyyar dasu ka yi rijista a lokacin aikin rijista da sabunta katin jam’iyyar a jihar da kuma wurin tsarin fiddo da wakilan da zasu zabin yan’takara.
Ya tunato cewa yin amfani da tsarin sasanci wajen zaben shuwagabannin jam’iyyar a jihar yace matakin yak taimaka wajen hana bata lokaci warin zaben shuwaga bannin jamiyyar.
Shugaban kwamitin ya ce za a gabatar da cikakken rahoton ga uwar jam’iyyar ta kasa dake Abuja.
Da yake mayar da jawabi gwamnan jihar Aminu Bello ya yaba ma kwamitin bisa yadda suka kammala aikin su akan lokaci.
Gwamnan ya kuma gode ma kwamitin bisa yadda suka bi dokar zabe wadda ta tanadar cewa wajibi ne a mika ma hukumar zabe jadawalin sunayen wakilan zuwa juma’ar data gabata.
Tun farko sakataren gwamnatin jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal ya ce kwamitin ya zo ofishin gwamnan ne domin gabatar da rahoton wucin gadi da ya shirya mika shi ga uwar jam’iyyar APC ta kasa.