Shugabanci Na Gari Shi Ne Adalci — Masari.
Daga Auwal Isah
Gwamnan jihar Katsina ya ce matakin samun shugabanci na gari shi ne adalci.
Aminu Bello Masariya fadin hakan ne a lokacin da sabbin jami’an kungiyar Christoci ta Najeriya reshen jihar Katsina suka kawo mashi ziyarar ban girma.
Gwamnan ya karfafa gwiwar sabbin membobin kungiyar da cewa su rika yin shigar mutumci don ganin al’ummomin da suke cikin suna mutumta su.
Gwamna Aminu Bello Masari ya bada tabbacin cewa, gwamnatin jiha za ta taimaka ma kungiyar don ganin ta cimma abubuwan da ta sa gaba.
Tunda farko, saida sabon shugaban kungiyar Reverend Richard Shu’aibu ya bada tabbaci goya ma manufofi da shirye shiryen gwamnati baya.
