Azumin Ramadan: Saratu Giɗaɗo Ta Yi Kira Ga Mawadata.
Daga MUKHTAR YAKUBU.
Fitacciyar jaruma a Masana’antar Kannywwod Hajiya Saratu Gidado, wadda aka fi sani da sunan Daso, ta yi kira ga mawadata da su duba yanayin halin da mutane suke na kuncin rayuwa musamman a wannan wata na Ramadan mai albarka.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar da muka yi da ita a game da shirin da ta saba yi a duk shekara na ciyar da mabuƙata a duk watan Ramadan idan ya zagayo in da take dafa abinci kullum da yamma a ke rabar da shi ga mabuƙata a lokacin buda Baki.
Haka kuma jarumar ta ce “A bana an samu sauyi sosai a kan yadda na saba yi a duk shekara. Domin a baya na kan dafa abinci ne kullum da yamma a raba wa jama’a domin su yi buɗa baki da shi a lokacin shan ruwa.”
Ta ƙara da cewar “Sai dai a wannan shekara ba kamar yadda na saba yi a baya ba da nake yi a kullum, domin kuwa a yanzu sai juma’a Juma’a zan rinƙa yi in dai ba na samu gudummawa daga jama’a ba domin yanayin da a ke ciki ya sa ba ni da karfin da zan rinƙa ciyarwa a kullum.
Don haka sai ta mayar da abin sati sati, saboda bata da karfi, kuma daman baya ga kuɗin da take kashewa a aljihunta, to tana samun gudummawa daga jama’a, amma dai a wannan karon har yanzu bata samu ba sai da dan abin da yake hannu ta take yi shi ya sa ba na samun damar yi Kullum “.
Daga karshe Saratu Gidado ta yi kira ga masu hali su bayar da gudummawar su domin ta samu damar ciyarwar da ta saba yi Kullum, don haka idan ana son a hada hannu da ita don ci gaba da yin wannan aikin na alheri, sai a nemeta Kai tsaye domin ba ta gudummawar,don tallafa wa mabukata.
