September 17, 2026

Ayyukan Cigaban Mazaɓu: An Yaba Da Ƙoƙarin Hon. Zakari Ya’u Galadima

0

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

An yaba da kokarin dan majalisar wakilai, mai wakiltar kananan hukumomin Bade da Jakusko a zauren majalisar wakilai ta Tarayya, Hon. Zakari Ya’u Galadima bisa ga kokarin samar da ayyukan ci gaba da raya mazabarsa, ta hanyar aiwatar da ayyukan da suka shafi inganta rayuwa da walwalar jama’a a fanni daban-daban.

Al’ummar sun bayyana matakin dan majalisar abin a yaba tare da jinjina masa saboda yadda ya jawo hankalin Gwamnatin Tarayya wajen kawowa al’ummar yankin dauki tare da aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban yankin tare da inganta rayuwar jama’a da tattalin arzikin su.

Wannan yabon ya fito ne daga bakin al’ummar kananan hukumomin Bade da Jakusko da ke jihar Yobe, sun bayyana hakan a lokacin da Hon. Galadima ya kaddamar da raba tallafin injinan noman rani ga manoma domin bunkasa harkokin noma tare da tallafa wa mata da na’urorin firiji domin yin sana’o’in dogaro da kai, a makon da ya wuce a garin Gashuwa da Jakusko.

Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun bayyana matikar godiya dangane da kokarin dan majalisar wajen kawo abubuwan ci gaban yankin tare da yadda suka nuna cewa tallafin zai bunkasa walwalar rayuwar su ta fannin inganta sana’a da noma a yankin. Yayin da suka kara da cewa, “Wannan tallafin ya zo daidai lokacin sa sakamakon irin yadda ambaliyar ruwa ta tagayyara rayuwar jama’ar wadannan kananan hukumomi. Mun yaba sosai dangane da wannan tallafin.”

Hon. Ya’u Galadima ya raba wa manoma a mazabarsa tallafin injinan noman rani 50 domin su inganta ayyukan noma don samar da isasshen abinci a yankin tare da raba wa mata firjuna 50 domin su samu sana’o’in dogaro da kai, a kananan hukumomi na Bade da Jakusko. Inda mata da dama sun nuna Ala-san-barka tare da matikar farinciki da godiya ga dan majalisar.

Har wala yau kuma, Hon. Zakari Ya’u Galadima bai tsaya a nan ba, inda ya yi kokari wajen hana jama’ar sa kasancewa cikin duhu ta hanyar sanya fitilun haskaka layuka (Street Light), masu amfani da hasken rana (Solar Power) guda 40 a mazabar Bade da Jakusko tare da sanya wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Gwio Kura, da samar rijiyoyin burtsatse masu na’urorin bayar da haske mai amfani da rana guda 7 a mazabarsa.

Al’ummar wadannan yankuna sun bayyana cewa wakilcin Hon. Zakari Ya’u Galadima a zauren majalisar wakilai ta Tarayya, kwalliya ta biya kudin sabulu, sakamakon yadda ya aiwatar musu da ayyukan raya mazabu wadanda suka shafi kowane bangaren ci gaba da inganta rayuwar al’ummar yankin sa dake birane da karkara.

Haka kuma, ya bai wa daruruwan matasa horo kan sana’o’i hannu daban-daban domin dogaro da kai, raba wa daruruwan matan karkara da birane kekunan dinki da injin markade hadi da tallafin kudi domin fara kananan sana’o’in dogaro da kai.

Bugu da kari, jama’ar sun nuna cewa wadannan ayyukan da dan majalisar ya aiwatar a matsayin abin a yaba saboda yadda suka yi daidai da bukatun su na yau da kullum. Sun bayyana samar wa matasa ayyukan yi da sana’o’in dogaro da kai a matsayin babban hangen nesa tare da dora matasan kan kyakkyawar turba da dakile zaman kashe wando.

Sannan sun yaba da aikin gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana hadi da gyara wadanda suka lalace a yankin domin samar da isassun ruwan sha.

Hon. Galadima ya nemawa matasa da dama aikin gwamnati a matakai daban-daban a fadin Tarayyar Nijeriya tare da samarwa wasu karin matasa tallafin karatu, gyara ajujuwa a makarantu, raba kayan karatu da makamantan su, domin bunkasa harkokin ilimi a yankin dama a jihar Yobe baki daya.

A hannu guda kuma, Hon. Ya’u Galadima ya gina sabuwar Cibiyar Sadarwa ta zamani (ICT) a garin Amshi domin sada yankin da sauran yankuna na duniya a harkokin sadarwa na zamani.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *