Yan Sanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka yi Garkuwa Da Su A Katsina
Rundunar ‘Yan Sanda ta tabbatar da kuɓutar da mutane 21 daga cikin 30 da ‘ yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Bayanin haka na kunshe a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar jiya asabar ta hannun kakakin ta SP Gambo Isah wanda kuma aka rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun yi nasarar kuɓutar da mutane ashirin da ɗaya da aka sace a gona suna aiki a kauyen mai lafiya da ke cikin ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Haka kuma kakakin rundunar ya bayyana cewa tuni suka miƙa waɗanda aka kuɓutar zuwa ga iyalansu domin cigaba da rayuwar su kamar kowa.
Kazalika rundunar ta ce ana cigaba da yin bincike gane da wannan al’amari mai matukar tada hankali, kuma da zaran an kammala za a sanar da jama’a.
Idan za a yi tunawa a satin da ya gabata ne ‘ yan bindiga ɗauke da muggan makamai suka kewaye wata babbar gona a kauyen mai lafiya inda suka kwashe mutane 30 sannan suka nemi kudin fansa Naira miliyan 30.
