Sadiq Zazzaɓi Ya Kai Ziyara Ga Khalifan Ƙadiriya Na Afrika.
Fitaccen mawakin siyasa Alhaji Sadiq Zazzaɓi ya kai ziyarar ban girma ga shugaba kuma Khalifan ɗariƙar Ƙadiriya na Afrika Sheikh Dr. Karibullahi Nasiru Kabara.
A lokacin wannan ziyara mawaki Sadiq Zazzaɓi ya mikawa shehin malamin wata sabuwar waƙa da ya yi wa shugaban halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam.
Sannan ya yi wa Marigayi Maulana Amirul Jaish Malam Nasiru kabara waƙa a duk cikin wannan faifan CD na waƙa da ya gabatar.
Daga shafin Sadiq Zazzaɓi
