September 17, 2026

Anya Kuwa Da gaske Gyara Suke So, Ko Dai Wata Ɓoyayyar Manufa: Zauren ‘Yan APC A Gyara

0

Daga Muhammadu Bello

Duk dai Hausawa na cewa gyara kayanka bai zama sauke a raba ba, kwatsam aka yi gari a jihar Katsina aka samu wasu tsirarun matasa da suka kira kansu Zauren APC A Gyara kuma sun kira kansu masu son kawo gyara da kishin Jam’iyyar APC shi ne babban dalilin kafa wannan zaure a jihar Katsina.

Amma abun tambaya anan shi ne shin dagaske gyaran suke so? Kuma wadanne hanyoyi suka biyo na ankarar da gwamnatin jihar Katsina da Jam’iyyar APC ta jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Alhaji Sani Aliyu Daura, wanda suka yi ko kuwa akwai wata boyayyar Manufa?

Jam’iyyar APC ta jihar Katsina ta kammala zaɓukan Fidda-gwaninta a matakai daban-daban ba tare da nuna banbanci ba, wadda a tarihin siyasar jihar Katsina ba’a taɓa samun haka na baiwa yan takara dama su nemi Jama’a tare da kokarin baiwa kowa damarsa ta dan Jam’iyya.

A Zaɓen Fidda-gwani gwamna da aka gudanar gwamna Aminu Bello Masari ya yi kokarin matuka don gani an baiwa kowa damarsa ba tare da nuna Dan Bora da Mowa ba, wanda da yawa Jama’a sun yadda da sahihanci yadda aka gudanar da zaben. Yanzu haka babu wani korafi gaban kotu.

Amma kwatsam sai ga Waɗannan matasa sun fito da rana tsaka suna kira a Gyara to gyaran yadda aka gudanar da zaben Fidda-gwani da mafi yawancinsu wadanda suke goyawa ma baya, sun tsaya takara a matakai daban-daban, Allah bai ba su nasara ba, shi ne saboda Allah suke so a zo gyara, don uwayen gidansu ba su samu nasarar ba, ina da tabbaci da ace Iyayen gidansu sun yi nasarar lashe zaɓukan da suka tsaya da babu daya daga cikinsu zai fito ya ce a Gyara!

Idan muka koma tafiyar da gwamnati, gwamna Aminu Bello Masari yau shekararsa bakwai yana tafiyar da gwamnati a jihar Katsina. Tsakani da Allah cikin Waɗannan shekaru ba su taba fitowa da wani Zauren APC A Gyara sai yanzu da bai wuce saura watanni wa’adin Gwamnatinsa. Anya kuwa da gaske gyara suke so kuwa?

Kamar yadda da yawa daga cikinsu sun bayyana cewa tare da su aka sha wahalar aka kafa gwamnatin Gwamna Masari a shekarar 2015, ba su taɓa sunsunar kafa wannan zaure ba, saboda Allah fa al’umma jihar Katsina ku yi mana alkalanci! Amma suka yi gum da bakunansu.

Maganar shugaban Jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Sani Aliyu JB kuwa duk tsohan dan Jam’iyyar APC ya san irin rawar da ya taka, saboda shi ne Sakatarenta na farko daga likkafarsa ta cigaba ya zama shugabanta a shekarar 2021.

Duk wanda ya matsa kusa da shi mutum ne mai amsar gyara da kuma kokarin ganin an tafiyar da Jam’iyyar cikin adalci. Ina da yakinin cikinsu babu wanda ya taɓa kokarin yin mu’amalla da shi ko shigar da wani korafi na kawo gyara ace ya hau teburin na ki ba. Idan za ka yi adalci, farko ka fara kusantarsa kafin ka yanke masa hukunci.

Ni da a fahimta ta ko dai suna da wata boyayyar manufa, wadda nan gaba kadan al’ummar jihar Katsina za su fahimci haka. Yanzu dai babu abinda Gwamnatin Jihar Katsina da Jam’iyyar APC ke bukata, illa hadin kai yayan Jam’iyyar, ga zabe na tahowa na 2023, idan har nasarar Jam’iyyar APC suke so kyau su zo su marawa Jam’iyyar Baya ganin ta lashe zaɓukan, sannan duk wani gyara a zo ayi shi.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *