Ukraine Ta Nemi Goyan Bayan Kasashen Afrika.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya nemi goyan bayan Najeriya, Cote D’Ivoire dama sauran ƙasashen Afrika a fadan da kasar ke fama da shi, inji Popular News Hausa.
A kokarinshi na haɗa dangantakar tattalin arzikin da ƙasashen na Afrika, Zelensky ya ce, ya tattauna da shugabannin kasashen Afrika da dama, da suka haɗa dana Najeriya da kuma Cote D’Ivoire.
A lokacin wani taro da aka yi a zamance, shugaba Zelensky ya bayyana cewa zabu jarin kasar Ukraine a ƙasashen na Afrika zai bunkasa tattalin arzukin su dama kasar shi, da kuma samar da isashshen abinci ga kasashen.
Kamar yadda jaridar Popular News Hausa ta ruwaito, ya ce kasar shi nada kyakkyawar alaƙa dukkau da fadan data ke fama da shi, tare da bayyana cewa yana san yin kawance da kasashen Afrika don ganin Ukraine ta samu isashshen abinci.
Shugaba Zelensky ya kuma ce masana’antar sadarwa ta kasar Ukraine din za ta iya samar da damarmakin kasuwanci ga kasashen na Afrika.
Da yake yin tsokaci akan kawo karshen fadan da kasar ke fama da shi a halin yanzu, Zelensky ya ce ya dogara ne da lokacin da duniya za ta taimaki Ukraine din.
