Ana Cigaba Da Ɗaukar Fim Din Lu’u Lu’u Season 2 A Cikin Garin Katsina
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Yanzu haka an shiga kwana na uku a cigaba da ɗaukar shirin Fim din mai dogon zango wata Lu’ulu’u wanda darakta Aminu Mannir K’eza ke bada umarni.
Lu’ulu’u dai Fim ne da za a iya cewa kashi na farko ya samu karɓuwa a wajan masu kallo ta hanyar YouTube.
Haka kuma wannan shirin ya samu daukar nauyi daga matashin dan kasuwar nan kuma jarumi a masana’antar Kannywood Lawal A Agga wanda aka fi sani Bawan Mata.
Kazalika shirin lu’ulu’u yana samun kulawar Isa Bawa Doro domin ganin an samu nasarar shirin kamar yadda aka tsara.
Kamar yadda aka sani, kashi na farko na wannan Fim na lu’ulu’u yana dauke da manya da ƙananan jarumai da suka haɗa da na Katsina da kuma na jihar Kano.
Sannu a hankali wannan kafa ta Popular News Hausa zata ci gaba da kawo maku irin abubuwan da suke wakana a wannan dandali na daukar shirin Fim din lu’ulu’u.
Sannan idan dama ta bada zamu rike kawo maku hiraraki da jaruman da suka halarci daukar shirin Fim din da suka haɗa da na gida Katsina da kuma baki da suka zo daga nesa.
