September 18, 2026

An Shafe Kusan Kwana 180 Ba a Fuskanci Hara-haran ‘Yan Bindiga a Katsina Ba – Ibrahim Katsina

0

Biyo bayan kyawawan matakan tsaro da gwamna Aminu Masari ya ɗauka a jihar Katsina, jihar ta share sama da watanni 6 ba tare fuskantar ƙwaƙƙwaran harin ƴan ta’adda ba

Baban Mai baiwa gwamna Aminu Bello Masari shawara akan sha’anin tsaro Alhaji Ibrahim Muhammad Katsina Ya bayyana haka a Katsina

A cewar Ibrahim Katsina idan har za a yi adalci a faɗi gaskiya to hare haren da akayi ba za su wuce ɗaya ko biyu ba a jihar Katsina cikin wannan lokacin.

Ibrahim Katsina ya shaida haka ne a hirar sa da kafar sadarwa ta Jakadiya RTV a ofishin sa dake Katsina dangane da sha’anin tsaro a jahar.

Kakaki Network

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *