Yadda Yar’adua Ya Yi Ruwan Kudi Ga ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP A Katsina
Architect Ahmed Aminu Yar’adua Ya Bayar Da Gudummuwar Sama Da Naira Miliyan 13 Ga Yan Takarar PDP Domin Tunkarar Zaben Kananan Hukumomi
Tsohon Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina A Karkashin Jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2015 da 2019 Architect Ahmed Aminu Yar’adua, ya bayar da gudummuwar Kudi sama da naira Miliyan 13 ga Yan Takarar PDP domin Tunkarar Zaben Kananan Hukumomi dake tafe a Jihar.
Architect Ahmed Aminu Yar’adua ya mika gudummuwar kudin ne ga dukkan yan takarar Shugabancin Kananan Hukumomi da Kansiloli na Kananan Hukumomi 34 da Mazabu 361 da ke fadin Jihar Katsina.
Kamar yadda tsarin gudummuwar ta nuna, Kowane Dan Takarar Shugabancin Karamar Hukuma zai karbi gudummuwar naira 100,000, sai yan takarar Kansila da aka baiwa gudummuwar naira 20,000 kowannensu.
A dayan bangaren kuma, kowace Karamar Hukuma Architect Ahmed Aminu Yar’adua ya baiwa Jam’iyyar PDP naira 50,000, sai Shiyyoyi guda 3 da ake da su a Jihar suma ya basu naira dubu 100,000 kowannensu.
Bugu da kari Architect Ahmed Aminu Yar’adua ya kuma baiwa Uwar Jam’iyyar ta jiha naira dubu 500,000.
Kamar yadda Architect Ahmed Aminu Yar’adua ya bayyana, tallafin kudin nada nufin bayar da dama ga Jam’iyyar domin ta tunkari zaben Kananan Hukumomi da ke tafe a wannan shekara ta 2022.
Tsohon Mai neman takarar ya nanata kudirinshi na cigaba da kasancewa mai biyayya da bada gudummuwa ga Jam’iyyar domin samun nasararta a dukkan matakai.
A nashi jawabin,Shugaban Jam’iyyar na Jihar Katsina Alhaji Salisu Yusuf Majigiri, ya nuna farin ciki akan wannan gudummuwa da Architect Ahmed Aminu Yar’adua ya bayar.
Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya tabbatar da cewar tallafin zai kara kwarin gwuiwa ga Jam’iyyar domin ta tunkari zaben na Kananan Hukumomi a Jihar.
Sauran wadanda suka maganta sun hada da Honarabul Sirajo Ibrahim Karare da da Alhaji Aminu Bello Kofar Bai da dai sauransu.
A madadin yan takarar da suka amfana,Dan Takarar Shugabancin Karamar Hukumar Kurfi Farfesa Abdulkadir Kurfi, ya yabawa Architect Ahmed Yar’adua akan Tallafin.
The Fact 24
