An Gudanar Da Taron Wayar Da Kan Mata Akan Muguwar Aƙida A Kano
Daga Babangida Sunusi, Kano
a ranar alhamis din data gabatane aka gudanar da taron wayarma da mata kai dan kaucewar aqida dake jan ragamar lalata rayuwar al’umma ajahar Kano.
Taron wanda ya gudana a dakin taro na afficent dake a GRA karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano da nufin tunawa da ranar mata ta duniya da aka gudanar makon jiya yasamu halartar mata daga yankuna daban daban na hukumomin tsaro da kungiyoyin mata da masu zaman kansu.
Da yake jawabi tun farko yayin taron shugaban kungiyar wanzar da domokuradiyya Mai dorewa Dr Muhammad Mustapha,yace sun hada wannan taron ne dan ganin mata amatsayin iyaye Kuma masu bada tarbiyya ga al’umma tare da kulawa yakarama masu kaimi wajen wayar masu da kai dan kaucewa matsalolin daka iya faruwa.
Dakta Muhammad Mustapha yakuma kara bayyana cewa lallai yanzu ne lokacin da yakamata akara wayarma da mata kai dan su kokarta ganin yadda zasu tsame ya’yan su damu kanmu wajen shigar da matasa da sauran mutane cikin mugayen kungiyon akidu na kashe kashe da shaye-shaye dake wanzuwa ahalin yanzu.
Dakta ya kumayi qarin haske kan irin abubuwan dake wanzuw awasu kasashen dake nesa damu yazuwa kusadamu wanda ayanzu Kuma sun matso kusa damu harda makwabtan jahohinmu nakusa na tashin hankali da gurvacewar tarbiya.
Babban daraktan yakuma tabbatar da cewa kasancewar rashin isasun jami’an tsaro da kasarmu take fuskanta yanzu,yazama dole mukasance jami’an tsaro mazan mu da matan mu,duk da cewa Suma mazan suna basu irin wannan bita,amma Suma matan akwai rawar da yakamata ace sun yaka yasa ake masu irin wannan bitar dan kara wayarmasu dakai kan matsaloli da illolin shiga irin wadanna kungiyoyi na koma baya.
Dr. yacigaba dacewa idan akai duba yanzu haka za’aga cewa ana kashe iyaye maza Wanda ke jefa mata cikin want mugun yanayi tareda barmasu ya’ya dabasu iya tsawatarwa da tarbiyyantarwa wanda yazama dole akula da wannan yanzu da wayarmasu da kai, wajen kaucewa shaye-shaye da karuwanci da mahimmanci shugabanci acikin al’umma.
Anashi jawabin shima ko’odineton action aids nakasa Mr Anicetus Atakpu yace sun fara gudanar da wannan aikin ne wasu daga cikin kananan hukumomin jihar Kano kamar karamar hukumar Bichi/Danzabuwa, Gwale/Dorayi,TudunWada/Yaryasa,Kofa da Gwarmai a karamar hukumar Bebeji, Brigade da Gama aqaramar hukumar Nasarawa.
Mr Anicetus Atakpu yakuma tabbatar dacewa bukatarsu anan shine mata suzama Suma ana damawa dasu wajen kawo chanji acikin harkokin yau da kullum.
Kazalika wannan taro zai kara taimakawa wajen yadda Za’a taimaki jama’a mata da matasa ta hanyar da zasu taimaki kansu dawata sana’a dan rage samun mata cikin muguwar akidan dake janyosu cikin want aikin dakeda matsaloli.
Itama Dr Binta Abba dake sashen ilimi na jami’ar Bayero Kano data gabatar da takarda,tace ta tsaya gaban matanne dan kara taimakama mata wajen yadda zasu magance matsaloli ra’ayin rukau dan dakilesu wannan dabi’a.
Dr Binta Abba takuma ce yakamata ace mata sun san yadda ita wannan ra’ayin rumau take, da gano yadda za’a maganceta sannan Kuma taya gwamnati jahar kano zata taikama wajen magance ta.
Haka Kuma takuma mara dacewa tayaya kungiyoyi masu zaman kansu irin wadannan zasu kara taimakawa wajen magance wannan tabi’a, inda tace wannan dabi’a ba sabuwa bace ta dade kama daga yankin adini da al’ada dama siyasa indai zai iya kawo tashin hankali ko savanin zaman lafiya ga al’umma.
Itama malama Tasalla chibok wadda Mai bada shawara a kungiyar action aids dake Abuja yace sun taru anan ne dan samo mafita daga matsalar dake addabar mata wajen tsunduma harkar ta’addanci da shaye shaye ajahar Kano dama kasa baki daya.
Takumace lallai wannan lokaci yakamata ace mata sunfita lokacin zaben nan dan zavar Wanda yakamata tare da fitowa Suma ayi dasu aharkokin yau da kullum.
Hajiya Halima Bin Umar wadda Darakta a WIM ta nuna matuqar farin cikinta yadda aka shirya wannan taro.
Takumace yakamata mata sun tashi dan ganin andama dasu tare da jin tsoron Allah cikin al’amuransu na yau da kullum,tace kuma yadda akai maganar yadda iyaye zasu tarbiyya dan samun raguwar matsaloli tareda kaucewa san zuciya.
Daga karshe an kuma gabatar da sana’o’i daban daban da duk macen dake bukata ta koya zata iya zaba tareda bada sunanta dan yin rajista
