Hon. Haruna Musa Yar’adua Ya Amsa Kiraye-kirayen Fitowa Takarar Majalisar Tarayya Ta Katsina Ta Tsakiya
Babban Mai Taimaka Wa Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Haruna Musa Da Aka Fi Sani Da (Sahu Ya Daidaita) Ya Amsa Kiraye-kirayen Da Al’ummar Jihar Katsina, Musamman Na Mazabar Katsina Ta Tsakiya, Inda Ya Amince Da Fitowa Takarar Dan Majalisar Wakilai A Mazabar Katsina Ta Tsakiya A Zaɓen Shekarar 2023 Mai Karatowa.
Honarabul Haruna Musa Yar’adua Ya Bayyana Haka Ne A Lokacin Da Ya Ke Tattauna Wa Da Manema Labarai A Yau Lahadi.
Mataimaki Na Musamman Kuma Daya Daga Cikin Na Hannun Damar Gwamna Aminu Bello Masari Ya Bayyana Cewa Ya Fito Takarar Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Karamar Hukumar Katsina A Zauren Majalisar Wakilai Ta Kasa Domin Cigaba Da Inganta Rayuwar Matasa Da Mata Da Kuma Masu Karamin Karfi. Zan Kuma Jajirce Wajen Ganin Na Samarwa Matasa Wannan Mazabar Aikin A Ma’aikatu Da Hukumomin Gwamnatin Tarayya, Idan Allah Ya Ba Mu Nasarar.
Alhaji Haruna Musa Yar’adua Ya Kara Jaddada Kuudurinsa Na Ganin Matasa Sun Samu Horo Da Kuma Kwarewa Kan Kasuwancin Zamani Wanda Za Su Zama Masu Dogaro Da Kansu.
Honarabul Haruna Musa Yar’adua,Wanda Shine Darakta Janar Na Kungiyar Nan Ta Sahu Ya Daidaita Ya Bayyana Cewa Kuma Zai Fito Takarar Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Karamar Hukumar Katsina A Karƙashin Jam’iyyar APC Domin Cigaba Da Kawo Canji Mai Ma’ana Wanda Zai Karade Lungu Da Saƙon Wannan Mazabar. Wannan Tafiya Ta Matasa Da Da Masu Karamin Ƙarfi Da Mata.
