An Buƙaci Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ƙara Maida Hankali Ga Cigaban Addinin Muslunci.
An Buƙaci Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ƙara Maida Hankali Ga Cigaban Addinin Muslunci.
An buƙaci gwamnatin jihar Katsina ta ƙara maida hankali ga cigaban addinin Muslunci domin amfanin al’ummarta.
Babban jojin jihar Katsina Musa Danladi Abubakar ya yi wannan kiran a lokacin walimar yaye ɗaliban makarantar Madarasatul Nurul Huda Sabuwar Kofa cikin garin Katsina.
Ya bayyana cewa, akwai bukatar gwamnati ta cigaba da zuba kuɗi domin bunƙasa ilimin addinin Muslunci.
Musa Danladi Abubakar ya kuma ja kunnen iyaye su tabbatar da ƴaƴansu na amfani da kafar sada zumunta ta zamani domin neman ilimin da zai amfane su a duniya da lahira, madadin amfani da ita ba yadda ya kamata ba.
A nashi ɓangaren, Sarkin Sulluɓawan Katsina hakimin Kaita Yazidu Abdulkarim Kabir Usman ya shawarci iyaye su kula da a lokacin zuwa makaranta dama bayan lokacin makarantar.
Tunda farko, daraktan makarantar Malam Abubakar Alkasim Farin Yaro ya bayyana cewa, a kafa makarantar ne a shekarar 1979, kuma yanzu tana da ɗalibai sama da 1,600.
Ya yi kira ga Musulmi masu kishi su taimaka ma Islamiyyar domin ganin ta ƙara cigaba.
