September 17, 2026

An Karrama Kwamishinan Kula Da Harkokin Noma Na Jihar Katsina.

0

An Karrama Kwamishinan Kula Da Harkokin Noma Na Jihar Katsina.

An gudanar da taron karrama kwamishinan kula da harkokin noma da dabbobi Farfesa Ahmed Mohammed Bakori a Bakori.

 

Masu ruwa da tsaki ne suka shirya taron karramawar karkashin jagorancin Mariya Abdullahi da Shehu Mamman Bakori.

 

Mariya Abdullahi ta ce al’ummomin Bakori sun yanke shawarar karrama kwamishinan ne bisa la’akari da ƙoƙarinshi ga bunƙasa zaman lafiya da cigaban yankin.

 

Mariya ta bayyana kwamishinan a matsayin mai hangen nesa, wanda ya bada fifiko ga bunƙasa rayuwar matasa da tattalin arzikin ƙaramar hukumar Bakori.

 

A tsokacinshi, sakataren kwamitin shirya taron karramawar, shehu Mamman Bakori ya ce kwamishinan na taimaka ma mutane, tare da buƙatar shi da cewa kada yayi kasa-a-gwiwa a ƙoƙarin shi ciyar da yankin gaba.

 

A jawabinshi, shugaban ƙaramar hukumar Bakori Ali Maicitta ya ce, ƙaramar hukumar a shirye ta ke tayi aiki da dukkan wanda ke shirin kawo ma yankin cigaba.

 

Shima da yake magana, kwamishinan bunƙasa rayuwar matasa da harkokin wasanni Aliyu Lawal Shargalle ya shawarci kwamishinan ya cigaba da ƙoƙarin ganin ƙaramar hukumar ta cigaba.

 

A tsokacinshi, Jarman Katsina hakimin Tsiga Dikko Tukur ya yi kira ga kwamitin ya shirya taron ƙara ma juna sani ga sauran mutane a yankin da suka yi fice a bangarori daban daban.

 

Da yake maida jawabi, wanda aka karraman, wanda kuma shi ne kwamishinan kula da harkokin noma da dabbobi Ahmed Mohammed Bakori ya bada tabbacin yin bakin ƙoƙarinshi domin cigaban yankin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *