September 18, 2026

Akeredolu Ya Saki Fursunoni 7, Sanwo-Olu Ya Saki 104.

0

A jiya Lahadi ne 1 ga watan shekarar 2023 gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, ya yi afuwa ga fursunoni bakwai da ke zaman gidan yari daban-daban, domin murnar shiga sabuwar shekara.

Babban mai shigar da ƙara kuma kwamishinan shari’a na jihar, Charles Titiloye ya bayyana cewa gwamnan ya kuma rage wa’adin zaman gidan yari na wasu fursunoni 11 a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Titiloye ya ce: “Wannan matsayar gwamnan ta biyo bayan shawarar majalisar bada shawarwari ta jihar akan tausayawa wadda ta ce, fursunonin sun samu horo a gidan gyaran halin, inda yanzu haka ma suka zama masu halin kirki.”

“Gwamnan ya kuma rage wa’adin zaman gidan yari na fursunoni 11.

“Bakwai daga cikin fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya, an mayar da hukuncin nashi zuwa na daurin rai da rai, yayin da aka rage shekarun daurin sauran fursunoni hudu.”

Sanwo-Olu ya saki fursunoni 104

Hakazalika, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, a jiya, ya bayar da umarnin sakin fursunoni 104 a gidajen yari guda biyar dake jihar.

A wata sanarwa da babban mai shigar da kara kuma kwamishinan shari’a na jihar, Moyosore Onigbanjo, SAN, ya fitar, gwamnan ya sanya hannu kan takardar sakin ne a ranar 28 ga watan Disamba bisa shawarar majalisar ba da shawara kan jin kai.

Onigbanjo ya ce: “Majalisar ba da shawarar ta dogara ne da bayanan da hukumomin gidan yarin suka bayar da suka haɗa da, yanayin laifin da fursunonin suka aikata, tsawon lokacin da suka kwashe gidan yarin, shekarun haihuwarsu, bayanin lafiyarsu da kuma halayensu, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Vanguard.

“Amincewa da sakin fursunonin ya yi daidai da alƙawarin gwamnatin jihar Lagos din na rage cinkoso a gidajen gyaran halin jihar, wanda ke cikin matakin sake fasalin sashin shari’a.”

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *