September 17, 2026

An Bude Sabon Masallacin Juma’a A Batagarawa, Katsina.

0

Sarkin Katsina ya yi kira ga al’ummar Musulmi su daga darajar addinin Musulunci.

Abdulmummuni Kabir Usman ya yi wannan kiran ne a lokacin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da aka gina a Ajiwa cikin karamar hukumar Batagarawa.

Ya bayyana bukatar ganin malaman addinin Muslunci na yin wa’azi domin samun zaman lafiya da hadin kai.

Sarkin ya kuma yi addu’ar ganin an gudanar babban zaɓen dake lami lafiya.

A tsokacinshi, shugaban kungiyar Munazzzama na jiha Sheikh Ishaq Nuhu Batagarawa da ya yi bayani ta bakin sakataren kungiyar Malam Ibrahim Gora ya bayyana mahimmancin neman ilimin addinin Islama dana Boko, da kuma mahimmanci gyaran makarantun Islamiyya da masallatai.

A jawabinshi, malam Labaran Iman Saulawa ya bayyana mahimmancin kula da makarantu da masallatai, tare da shawartar su ba sabon limamin shawara haɗi da yi mashi addu’a domin ganin ya sauke nauyin dake kanshi.

Daga karshe dai, mataimakin babban limamin masallacin katsina Malam Dayyabu Liman ya limancin salla raka’a 2, kuma sarkin Katsina ya naɗa Malam Salmanu Sani a matsayin sabon limamin a masallacin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *