Abubuwa Biyu Ne Suka Sa Na Fito Takarar Gwamnan Jihar Katsina – SGS Mustapha Inuwa
Daga El-Zaharadeen Umar
Mai neman takarar kujerar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyar APC Dakta Mustapha Inuwa ya bayyana dalilan da suka sa ya fito takarar gwamnan jihar Katsina a kakar zaɓe mai zuwa ta 2023
Dakta Mustapha Inuwa yana wannan bayani ne a lokacin da yake zantawa a wani shiri na gidan rediyon vision FM Katsina mai suna Babar Magana a yau Alhamis.
Ɗan takarar ya bayyana cewa an fahimci ya yi wasu ayyuka a matakin ƙaramar hukuma da kuma jiha da ita kanta jami’yyar APC ya yi mata hidima bakin gwargwado.
Ya ƙara da cewa a dalilin haka yana da masaniya ciki da wajen jihar Katsina kuma ya yi aiki lokacin da gwamnati ke da kuɗi da kuma lokacin da gwamnati ke fuskantar matsalar kuɗi.
Abu na biyu a cewar sa shi ne jama’ar da yake tare da su, wanda kuma tun ba a yi nisa a zango na biyu na wannan gwamnati ba suka fara batun in ya yi takara.
“To amma saboda dalilai da dama ban amince ba, na farko dai ita kanta gwamnatin bata daɗe da yin zaɓe karo na biyu ba, kuma idan har aka shiga hidimar siyasa to ba mu yi wa shi kanshi mai girma gwamna Aminu Bello Masari adalci ba, kuma hukumar zaɓe bata fitar da ƙa’idoji ba, ita uwar jam’iyya bata sa lokaci ba, wannan yasa na naki amincewa da buƙatun su a wancan lokaci” inji shi
Dakta Mustapha Inuwa ya ce yanzu lokaci ya yi shi yasa na amsa kiran jama’a kuma zai kasance cikin masu neman wannan kujera, saboda haka ba ya fito ba wai dan a mutu ko ayi rai ba, idan shi ne alheri a jihar Katsina da al’umma Allah ya bashi in kuma akwai waɗanda suka fi shi zama alheri to Allah ya kawo.
