An Kashe Sojoji da Dan Sanda A Taraba.
‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar sojoji shida, da dan sanda daya a Taraba.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Taraba ta tabbatar da kashe jami’an soji shida da dan sanda daya a wani rikici da ya barke tsakanin wasu kabilu biyu a wani kauye da ke karamar hukumar Takum da ke jihar.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, DSP Abdullahi Usman ya tabbatar wa manema labarai rasuwar a ranar Larabar da ta gabata a babban birnin Jalingo na Arewa maso Gabashin Najeriya.
“Rikici ne ya barke a ranar Talata tsakanin Fulani da ‘yan bindigar Kuteb a kauyen Tarti da ke karamar hukumar Takum a jihar Taraba, inda aka kona gidaje da dama, wanda ya kai ga hakan” in ji DSP Usman.
A cewarsa, ba a ga kwamandan da ke jagorantar soji n ba a yankin na Terti, Laftanar-Kanar Eminike.
Ya ce rundunar ‘yan sandan jihar Taraba a karkashin jagorancin CP Abimbola Sokoya, ta aike da karin jami’ai domin kai dauki a yankin.
Majiyarmu ta FRNC ta ce, A halin da ake ciki, Majalisar Dattawa ta nuna jimamin kashe mutane sama da 40 da suka hada da sojoji da ‘yan ta’adda suka yi a kudancin jihar Tarabar.
Hakan ya biyo bayan gabatar da wani kuduri da Sanata Emmanuel Bwacha mai wakiltar Taraba ta Kudu ya yi.
