Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Dakatar Da Gudanar Da Shirin Nan Mai Farin Jini Na Idon Mikiya….
Bayanai da suke fitowa daga Gidan Radiyon Vision FM da kuma Farin Wata TV sun bayyana cewa Hukumar Gudanarwa ta Kampanin Vision Media Service ya samu saƙon Takardar dakatar da gabatar da Shirin Idon Mikiya bisa abinda akayi Ittifaƙin cewa sukar da akeyi ma Gwamnatin ne akan wasu daga cikin Ayyukan ta.
Kazalika wani Rahoton ya bayyana cewa an vi Tarar Gidan Rediyon vision FM dake Kano Naira Dubu Ɗari Ukku da Hamsin domin wani Shirin da Ɗan Bilki Ƙwamanda yayi Wanda yake chachakar Gwamna Ganduje.
