Masu Saida Abinci Ga Mustapha Inuwa: Muna Cikin Harkokin Dumu-Dumu.
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Hadaddiyar Kungiyar masu gidajan sai da abinci ta jihar Katsina ta nuna goyan bayan ta ga gwamnatin jihar Katsina da kuma sakataranta Mustapha Muhammad Inuwa inda ta ce suna cikin duk wasu harkoki da za su ta so, domin bada gudunamwarsu a matsayinsu na ‘yan jihar Katsina
Shugaban kungiyar na jihar Katsina, Alhaji Aminu Kabir Kofar Sauri ya bayyana haka a lokacin da suka kaiwa Sakataran gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ziyarar bar girma da kuma gabatar da kai a karon farko tun bayan kirkiran kungiyar.
Alhaji Aminu Kabir wanda ya ce wannan kungiyar ta su ta karade duk jihar Katsina baki daya kuma suna mambobi masu gidan abinci fiye da 150 a fadin jihar Katsina.
“Mai Girma Sakataran gwamnati mun zo nan ne domin gabatar da kanmu a wajanka, kuma muna son mu shaida maka cewa kungiyarmu tana tare da gwamnati Aminu Bello Masari da kai kanka, sannan muna son a bamu dama mu bada ta mu gudunmawar kasancewar ‘yan jihar nan” inji shi
Ya ce suna bada gudunmawa wajan samar da kudadan shiga ga gwamnati sannan suna taimakawa wajan rage masu zaman kashe wanda ta hanyar samarwa da matasa aikin yi, uwa uba ya ce suna koyawa mata wannan sana’a domin su yi a gidajan mazajan su.
Shugaban ya yi kira da cewa suna son a rika sanya su cikin harkokin gwamnati musamman wajan ba su aikin abinci idan anyi wasu baki wanda hakan zai taimaka wajan bunkasar kasuwancin su da kuma dorewarsa.
Da yake maida jawabi sakataran gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ya nuna jin dadinsa da ganin wannan kungiya wanda ya fara da taya su murnar kafa ta, tare da fadin cewa gwamnati na bukatar irie-iren wadannan kungiyoyi
A cewarsa ta hanyar kungiya gwamnatin na samun sauki haduwa da jama’a da dama, sannan ya ja hankalinsu akan su kara inganta sana’arsu domin ta haka ne za su kara bada gudunmawa da kuma samun karuwar arziki.
“Yin Abinci mai kyau da tsafta da kuma inganci yana taimakawa wajan rage kamuwa da cututuka, saboda wani lpkacin jama’a na kamuwa da cututuka ne ta hanyar abincin marar tsafta da inganci,” inji SGS
Ya kuma kara da cewa babu wata sana’a da Allah ya yi albarka kamar sana’ar saida abinci, sai ya kara da cewa duk gwamnatin da bata tallafawa masu irin wannan sana’a ba, lallai bata da akida tunda gwamnati bata iya ba kowa aiki, ita kuwa wannan kungiyar tana samar da ayyuka a jama’a.
“Ya zama wajibi mu taimaka maku, zamu duba ta inda za a tallafawa wannan kungiya ko hanyar bada bashi kuma shigar da kungiyar ta hanyar bada tallafi, sannan ya kara jadadda bukatar da ake da ita na kara inganta wannan sana’a ta sai da abinci a fadin jihar Katsina
