Shugaba Buhari Nasan Ayi Adalci AKan Kisan Hanifa Yarinya ‘yar Shekaru Biyar da Aka Kashe A Kano
Daga Awwal Isah, Katsina
A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga dukkan hukumomin da abun ya shafi da su tabbatar da an yi adalci akan lamarin kashe yarinyar nan mai suna Hanifa Abubakar ƴar shekaru 5 a Kano.
Ya umarci ƴan sanda da ma’aikatar shara’a da su tabbatar da ganin cewa an yi adalci akan lamarin ta hanyar gudanar da sahihin bincike, tare da gabatar da kyas ɗin gaban kotu yadda ya kamata.
Shugaban ƴasar ya bada wannan umarnin ne a cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun shi Malam Garba Shehu ya fitar, a tsokacin shi kan kisan yarinyarda aka yi, wadda aka yi garkuwa da ita a cikin watan Disambar shekarar da ta gabata.
Ya yi ta’aziyya a madadin ƴan Nigeria ga iyayen yarinyar, wadda bayan kashe ta, aka kuma bunne ta a cikin wani rami.
Kuma shugaban Nigeriar ya yaba ma jami’an tsaro bisa gudanar da binciken da ya tona asirin yadda yarinyar ta salwanta, wanda ya haɗa da kama malamin ta, da waɗanda ake zargi sun taimaka ma shi wurin yin wannan mugun aiki.
Kamar yadda ya bayyana, iyayen Hanifa, dama sauran ƴan Nigeria masu biye labarin ɓatan ta, sun ta sa ran ganin Allah ya maido ta cikin ƙoshin lafiya.
Shugaban ƙasa Buhari ya yi addu’ar Allah ya ji ƙan ta da rahama, tare da ba iyalan ta haƙurin jure wannan rashin.
