Dan Sandan Da Ya Kashe Wata Lauya, Bai Amsa Laifin Ba.
Dan sandan da ake zargin ya kashe wata Lauya a ranar Kirsimeti a Lagos ya ce bai aikata hakan ba.
An gurfanar da dan sandan mai suna Drambi Vandi a gaban wata babbar kotun jihar Lagos a wannan Litinin din, inda kuma ya ki amsa laifin kashe Mrs. Bolanle Raheem.
Sai dai kuma a lokacin da aka fara shari’ar, wani shaida ya baiwa babbar kotun jihar Lagos din cikakken bayani yadda wani dan sanda mai muƙamin ASP Mr. Drambi Vandi ya kashe wata lauya mai suna Bolanle Raheem a lokacin bukukuwan Kirsimeti.
Shaidan mai muƙamin insifekta da aka bayyana sunanshi a matsayin Matthew Ahmen dake zama abokin aikin Drambi Vandi da ya kashe lauyar, ya shaida wa babbar kotun da ke zamanta a Tafawa Balewa a ranar Litinin 17/01/2023 cewa, suna aikin tsaida ababen da bincike akan hanya a lokacin da lamarin ya faru.
Ya ce Vandi wanda shi ne shugaban tawagarsu yana baya, yayin da yake tsakiya, sai kuma wani abokin aikinsa, Insfekta Dimini na gaba.
Ahmen wanda shi ne shaida na farko mai gabatar da ƙara, ya ce a lokacin da Dimini ya ga wata mota tafe, sai ya yi kokarin tsaida ta, amma ba ta tsaya ba, kuma da motar ta nifi inda yake tsaye, ya sake tsaida ta, amma motar ba ta tsaya ba.
Ya ce: “Abu na gaba da na ji shi ne harbin bindiga, sai na waiwaya don in ga abin da ke faruwa sai na ga gilashin mota na zuba kasa.”
“Abin da na sake gani shi ne wata bakar mace ta fito daga motar, sai na ji tana cewa ‘oga ka kashe man kanwa.” Matar ta rike shi kuma kafin ni da Dimini mu isa wurinsu, sun shiga cikin motar, sun kulle, sun tafi, a cewar jaridar Sunnews majiyar jaridar Popular News Hausa.
