September 17, 2026

*GASAR MARUBUTA HAUSA NA SHEKARAR 2022 WANDA ALIYU MOHAMMED RESEARCH LIBRARY, GUSAU INSTITUTE (GI) KADUNA, NIGERIA KE SHIRYAWA*

0

Daga Kabir Yusuf Anka, Kano

Aliyu Mohammed Research Library, Gusau Institute Kaduna ke shirya wannan gasa, da kuma ba da kyaututtuka da wallafa labarai uku (3) da suka yi nasara don kara kaimi ga marubuta adabin Hausa.

Gasar da ake yin ta a kowace shekara, tana daukar siffa da tsari na kowane irin labari adabin Hausa.

A gasar wannan shekarar ta 2022 za a bude amsar tsakuren labaran marubuta  daga karfe goma (10:00pm) na daren Litinin *10/1/2022* har Karfe goma (10:00pm) na daren Alhamis *31/3/2022*.

Ga masu sha’awar shiga wannan gasar, ana bukatar marubuci ko marubuciya da su kiyaye da waɗannan ƙa’idoji da dokoki kamar haka:

*1*. Ana bukatar marubuta su aiko da tsakuren shafi goma na labarin da suke son shiga gasar da shi. Ka da ya gaza, ka da ya wuce.

Za a turo da shafi goma na tsakuren labarin zuwa ga adireshin emel kamar haka:

 *gusau.institute@gmail.com*

Ko

*info@gusauinstitute.com*

Za’a iya turowa ta WhatsApp: *+2349011476342*

*2.* Duk marubuci ko marubuciya da ba su kai shekara sha takwas (18) ba, ana bukatan da su turo da izinin ko amincewar  iyayensu na shiga gasar.

*3.* Za a turo da labari a tsarin taifin (typing) na Microsoft Word watau

(MSWord) mai shafi shafi. Ka da a turo da PDF.

*4.* Ba a yarda a turo da  wani rubutun ko labarin da aka riga aka wallafa ko aka buga ko rubutawa ta internet ko kuma ya fita a matsayin littafi, ko aka taba karantawa a daya daga cikin kafofin watsa labarai ko Internet.

*5.* Ba a yarda da satar fasaha, ta hanyan yin amfani ko turo da labarin ko rubutun wani marubucin daban.

*6.* Za a turo da tsakuren labari daga karfe goma na daren Litinin 10/1/2022  har zuwa karfe goma na daren Alhamis 31/3/2022. Za a sanar da waɗenda sukayi nasara a matakin farko ranar Juma’a 20/5/2022, Insha Allah.

*7.* Waɗanda suka yi nasara a zagayen farko na gasar, Dole ne cikakken labarin da za su turo a zagayen karshe na gasar ya kunshi kalmomi dubu arbain (40,000) zuwa arba’in da biyar (45,000).

*8.* Alƙalai za su yi la’akari da kyawun harshe, hawa da saukar labari, zube, amfani da ingantacciyar Hausa, amfani da karin magana da kuma tsarin rubutu wajen zaben waɗanda za su yi nasara a gasar.

*9.* Duk wanda ya shiga wannan gasar, to ya kwana da sanin cewa duk abin da alƙalan gasar suka zartar shi ne daidai kuma karshe babu daukaka kara.

*10.* Za a turo da ID Card mai dauke da hoto da kuma cikakken sunan mai shiga gasar, za a turo da shaidar watan haihuwa ko shekaru,  kuma za a turo da cikkakken adireshi.

*11.* Duk labarin da aka turo zuwa adireshi email ko WhatsApp, babu hurumin canza wa da wani labarin ko canza fasalin sa ko tsarin sa.

*12.* Ba a yarda wani ko wata daga cikin ma’aikatan Cibiyar Gusau Institute ko danginsu makusanta su shiga wannan gasa ba.

*Mun gode.*

(a sani: na ɗan yi gyara a ƙa’idojin rubutun)     

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *