September 17, 2026

Zaɓen 2023: Hon. Sani Ɗanlami A Saman Sikelin Nasara

0

Daga Abu Ahmad

A ya yin da zaɓen ‘yan majalisar tarayya da na shugaban ƙasa a Najeriya ya rage ƙasa da kwana 35 alamun nasara na cigaba da baibaye tafiyar Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ɗan takarar majalisar tarayya a Katsina ta tsakiya.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyi da magoya baya ke nuna ɗan takarar a matsayin hanyar mafita a zaɓen 2023 a ƙaramar hukumar Katsina.

Shin ko ya ya jama’a ke kallon wannan nasara da ke bayyana a jirgin yaƙin neman zaɓen sa da masoya ke yi masa ba dare ba rana, wannan ita ce tambayar da muka jefa a tsakanin masoyansa domin jin amsar.

Sai dai kuma bincike ya tabbatar da cewa Hon. Sani Aliyu Ɗanlami na iya cin zaɓen sa salin alin idan har wannan tafiya tasa bata samu tsaiko ba duba da irin ƙoƙarin da aka san shi da shi tun kafin yanzu.

Abubuwan lura game da Hon. Ɗanlami su ne yadda yake ƙoƙarin kyautata alaƙa tsakanin sa da jama’a da kuma cigaba da taimako musamman matasa, wanda hakan ke ƙara fitowa da manufofin sa na siyasa.

Yana daga cikin mutane ƙalilan da suke kallon nasara ba tare da wata barazana ba, amma hakan bai sa ya riƙe hannu yana jiran nasarar ba, ya ƙara dage damtse wajan neman alfarmar al’umma domin sake ba shi dama a karo na biyu.

Ya zuwa yanzu al’umma musamman Katsina ta tsakiya na jin irin manufofin da kudirori na zai maida hankali akan su idan ya samu nasara, ya taɓa riƙe wannan kujera da yake neman yanzu, an ga abin kirkin da ya yi, yanzu kuma an ji abinda yake so yin idan ya ƙara samun dama.

Idan za a yi tunawa Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya ƙaddamar da rundunar yaƙin neman zaɓen sa wanda shugaba kuma jagora Hon. Hamisu Gambo (Ɗan Lawan Katsina) yake yi wa jagoranci

Tabbatuwar nasara na ƙara bayyana a lokacin da aka rantsar da dakarun da za su shiga lungu da sako domin neman alfarmar al’umma su zaɓi Hon. Sani Aliyu Ɗanlami na jam’iyyar APC da sauran ‘yan takara a zaɓe mai zuwa.

Duk da irin ƙalubalan da ake kallo ya dabibaye wannan zaɓe na 2023 amma ta wata fuskar ana sa ran cewa Hon. Sani Aliyu Ɗanlami zai riga saura kwashe mafi yawan kuri’un da za a kaɗa

Ko ba komi, idan aka ɗora Hon. Sani Aliyu Ɗanlami da sauran ‘yan takara a sikelin samun nasara, me zai kasance amsa idan na barku ku masu karatu…?

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *