September 18, 2026

Gombe: Kungiyar Dalibai Ta Yi Zanga-Zangar Ƙarin Kudin Makaranta, Sun Ce Hakan Ya Na Korar Dalibai.

0

A wannan Alhamis din ne gamayyar kungiyoyin daliban arewacin kasa suka fito kan titi don nuna rashin amincewarsu da karin kudin karatu a jami’o’in gwamnati a kasar, tare da gargadin cewa hakan zai haifar da barin karatun dalibai.

Kamar yadda daliban suka bayyana, sun fito domin yin zanga-zangar ne a kewayen gidan Sarkin Gombe domin nuna rashin jin dadinsu bisa karin kudin makaranta.

Da yake jawabi a madadin daliban, babbar jami’in gamayyar kungiyoyin daliban ta ƙasa Emuseh Gimba Bokunga ta ce zanga-zangar ta yi daidai da burin kungiyar don samun ingantaccen ilimi ga daliban Najeriya.

Ta bayyana cewa kungiyar ta fito ne a Gombe domin jawo hankalin jama’a kan illar da ke tattare da ci gaban ilimi a kasar nan. “Wannan ya biyo bayan amincewar da gwamnatin tarayya ta yi na manufofin tattalin arziki da ya jawo wa ‘yan Najeriya wahala, a cewar majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sunnews.

“Mun ga abin takaici sakamakon wadannan tsare-tsare marasa kyau, yunwa ta dabaibaye miliyoyin gidaje, hauhawar farashin kayayyaki sun kawo wahalhalun rayuwa, mutane na rasa ayyukan yi, sana’o’i sun lalace, matasan Najeriya sun rasa fatan suke da shi na samun aikin yi, asibitoci cike da marasa lafiya daban-daban da basu iya biyan kudaden magani,” Emuseh ya ce.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *