Mutane Sama Da dubu 340,000 Ne Suka yi Rijistar Neman Tallafin Rage Raɗaɗin Corona A Katsina
Daga Awwal Isah, Katsina
Kimamin mutane dubu dari uku da arba’in ne suka yi rijista domin neman tallafi da gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata bayar domin rage radadin cutar korona da ta addabi duniya daga kananan hukumomin 34 na jihar Katsina
Jami’in shirin na jahar Katsina Aliyu Isah Girka ne ya bayyana hakan a lokacin gudanar da wani shirin bada horo ga jami’an shirin da ya gudana a tsohon gidan gwamnatin jahar Katsina.
Kamar yadda bayyana, jahar Katsina ita ce ta biyu mai yawan mutanen da su ka nemi tallafin a cikin ƙasar nan.
Kuma ya ce gwamnatin tarayya ce ta ɓullo da wannan shiri haɗin gwiwa da bankin duniya da nufin tallafa ma mutanen da kullen zaman gida na cutar Corona ya shafa.
Aliyu Girka ya ci gaba da bayyaba cewa, waɗanda su ka yi rijista ne ta hanyar amfani da wayoyin salular su za a tattara bayanan su.
Haka zalika, waɗanda su ka nemi tallafin ya zama dole su mallaki lambar BVN, da asusun ajiya na banki, da katin ɗan ƙasa, da dai sauransu.
Ya ce manufar hakan ita ce, a gudanar da shirin ta na’urar computer, tare da tabbatar da ganin cewa an yi shi bisa gaskiya.
Shugaban shirin ya kuma buƙaci maso tattaro bayanan mutane da su tabbatar da cewa sun ɗoko sahihan bayanai, saboda za a duba dukkan bayanan da suka tura zuwa ga shafin na SOCU.
