2023: Ya Zama Wajibi Mu Zabi Mutumin Kirki Da Zai Wakilci Sufaye A Siyasa -Darika Awareness
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Shugaban zauran wayar da kai Na Darika awareness na jihar Katsina, Alhaji Aminu Zubairu Unguwar Jaji ya bayyana cewa a wannan karon dole ne su tashin tsaye wajan ganin sun fadakar da al’umma musamman mabiya Darikar Sufaye domin yin abinda ya kamata a kakar siyasa mai zuwa.
Wannan jawabi yana zuwa ne a lokacin da kungiyar zauran Darika awereness da ke Katsina ta shirya taron kaddamar da shuwagabaninta a matakin shiyya da kuma kananan hukumar domin tunkarar kalubalan siyasa da ta ce an yi mata nisa tuntuni acikinsa.
Shugaban ya kara da cewa aikin matasan Darika ne su zabi wanda zai shugabance su a kowane mataki na siaysa, idan kuma ba haka ba to lallai za a turo wani ya shugabance su ko suna so ko basa so, saboda ya ce ya zama wajibi a canza dabi’ar a siyasance.
Alhaji Aminu Unguwar Jaji yana mai cewa wannan aikin ko samun nasara ba zai yiwowa ba sai da hadin duk wat zawiyya da ke Katsina domin aikin na al’umma ba na mutun daya, ana bukatar sa hannun kowa da kowa domin cimma nasara.
“Mun dauki tsawon lokaci muna bin iyayenmu shehunnai domin nasar da su halin da mabiya darikar sufaye suka shiga a dalilin rashin wadanda za su wakilce su a siyasa, kuma Alhamdulillahi sun fahim shi haka, sun kuma bada goyan bayan tare da addu’o’in samun nasara” inji shi
Ya kara da cewa sun shafe foye da shekaru biyar wajan tuntube game da wannan hali da mabiya Darikar sufaye suka shiga na rashin wanda zai wakilic su a gwamnatance, amma dai daga karshe sun samu nasara wanda ita ce ta haifar da wannan taro da suka shirya domin fara aikin gadan-gadan.
Shugaban wayar da Kan Zauran Darikar ya bayyaba cewa yana da kyau kasan wanda zai shugabance ka ko wanene kuma ya kasance kana da aminci da alaka mai kyau tsakaninka da shi, sannan ya ce a wannan karon dole ne su zabi mutumin kirki kuma dan darikar sufaye saboda suna da yawan da za su iya yin haka.
A karshen jawabinsa ya una mahimmacin yin katin zabe ga wadanda bai yi ba, inda ya yi kira ga sauran zawiyyoyi da ke Katsina akan lallai su tashi tsaye wajan ganin duk wanda bai yi katin zabe ba kuma ya kai shekara 18 da a tabbatar ta yi domin yakin dole sai da katin zabe.
Shima a nasa wajabin shugaban kwamitin amintatu na wannan zaure Sheihk Malam Hadi Balarabe ya bayyana cewa ayi amfani da wannan tafiya wajan samar da mutumin da zai hada kai al’umma ba wai raraba su ba.
Sheihk Malam Hadi ya kara da cewa idan aka duba sauran abokana zaman Muslmi ba haka suke tafiyar da sha’anin rayuwarsu ta yau da kullun ba, suna tafiya ne tare da san juna da kuma mutunta kowa da kowa saboda haka ya zana wajibi da mabiya darikar sufaye su yi abinda yafi wancan.
Sannan ya yi kira ga wannan kungiya da ta fito sabbin tsare-tsare da su hada kan tafiyar matasa baba tare da wani bambance-bambace ba, a yi tafiya guda bisa manufa guda domin cimma nasarar wannan baban aiki da aka sa gaba.
Malamai masana ne suka gabatar da jawabai tare da kasidu, daga cikin su akwai Farfesa Abdulaziz Ahmed Mashi daga sashen larabci na jami’ar Umar Musa Yar’adua da sauran Malmai da suka ta’aliki. Taron wanda ya gudana a dakin taro na sakatariyar malamai ta Jihar katsina tya samu halartar Babban limamin na Jihar katsina Sheik Mustapha Gambo, da Malamai da shehunnai daga Zawiyyoyi daban-daban na Darikar Tijjaniya a fadin jihar Katsina
