November 19, 2026

Asibiti Ta Farko A Katsina Da Mata Ke Duba Mata

0

FATIMA MEMORIAL MATERNITY AND CHILDREN CLINIC.

Nasha ganin mutane hausawa musulmi na nuna alhininsu na rashin Asibiti ta mata wadda komai matane ke gudanarwa, to ga alama wannan matsala ta fara kuranyewa.

Duk da tsanantar al’amurra sai ka samu akwai al’umma wadanda shirye suke su bada Gudummuwar su wajen taimakon Al’ummar su, Fatima memorial maternity and children clinic wata asibitice da aka bude kusan shekara 4 da suka gabata a unguwar sakwatarima bisa titin da zaya maida mutum shataletale na rahamawa katsina Nigeria, amma dayawa mutane basu san da itaba.

Ita wannan asibiti da wata bayyawar Allah mai kishin al’ummarta ta bude,maaikaciyar lafiyace data share shekaru a cikin aikin lafiya yanzu haka itace katsina state Coordinator a sashen takaita iyali, ita wannan asibiti data samar an sanya kayan aiki, na zamani sannan ana saukaka farashin biyan kudi har yafi na wasu asibitocin gwabanati.

Baban abin jan hankali tatatare da asibitin shine duk abinda za’a yiwa mace to macece yar’uwarta keyi. Ana ayyuka a Wannnan asibiti kamar haka:
-Karbar haihuwa

  • Awon ciki
  • Awon (Scanning)
    -Duba kanann yara da rashin lafiya ta mata
  • kaciya/shayi.

Wannan asibiti na da alaka da manyan lokitoci da asibitoci ta inda duk abinda yagaresu kai tsaye zasu tura ma asibitin da zata kula da wannan matsala..

Ga masu kishin da sha’awar iyalensu su rika ganin likitoci mata a matsalolinsu zasu iya ziyartar wannan asibiti. Ko su tuntubesu ta number waya 08036222527, 08031195711 FATIMA MEMORIAL MATERNITY AND CHILDREN. Asibitin mata da yara.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *